1. Idan har rashin tasirin harsashen jami’an tsaron Nigeria ya tabbata, haka nan idan har rashin tasirin harsashen ya tabbata a matsayin wata irin karama ce ga shi jagoran ‘yan bidi’ar shi’anci a Nigeria, to kuwa ya kamata su ma mabiya Shugaban, watau babban mataimakinsa wannan bakanon, da kuma ‘ya’yan shi Shugaban, da sauran daruruwan mabiyansa cikin addinin shi’anci wadanda harsashai suka kashe, ya kamata a ce su ma rashin tasirin harsashan ya zama karama a garesu; wannan shi ne abin da zai dace da hankalin mahankalta.

2. Lelle zai yi matukar wuya a hankalce a ce abin da yake cikin waki’a guda, kuma game da mutane iri guda masu imani da abu guda, a ce wai Allah Madaukakin Sarki Ya aiko da karamar kubuta a cikinsu, kuma saboda tsantsar wannan imani nasu, sannan kuma wai a ce mutum daya kawai daga cikinsu ya sami wannan karamar, amma sauran mutanen babu daya daga cikinsu da ya sami ita wannan karamar!!

3. Ku lura, babbar izinarmu a cikin wannan bayani namu shi ne: a lokacin da babbar girmamawar kubuta daga sharrin shugabannin kafuran Makka ta sauko wa Annabi mai tsira da aminci, to tabbas wannan girmamawar ta shafi babban abokinsa cikin Musulunci da Imani watau Abubakar Siddiq Allah Ya kara masa yarda. Haka nan Allah Ya girmama Annabi Musa tare da dukkan jam’arsa Ya ketarar da su tekun Maliya.

4. Allah muke rokon Ya kare mu daga sharrin karairayin ‘yan bidi’ah. Ameen.

3 Comments

  1. I’m curious to find out what blog platform you’re working with? I’m having some small security problems with my latest website and I’d like to find something more secure. Do you have any solutions?

  2. I discovered your blog site on google and check a few of your early posts. Continue to keep up the very good operate. I just additional up your RSS feed to my MSN News Reader. Seeking forward to reading more from you later on!…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *