1. A gurin Hanafiyyah duk wanda ya yi rubutu boroboro cewa ya saki matarsa toh shi ke nan ta saku ke nan, swaa’un ya yi niyyar sakinta ko kuwa bai yi niyyar sakinta ba, swaa’un takardar ta kai ga hannunta ko kuwa ba ta kai ga hannunta ba.

2. A gurin Malikiyyah wanda duk ya rubuta saki ga matarsa tare da niyyar sakin, toh tabbas ta saku ke nan swaa’un takardar ta shiga hannunta ko kuwa ba ta shiga hannunta ba, in kuwa ya rubuta sakin ne kawai ba tare da niyyar sakinta ba, toh in har takardar ta shiga hannunta toh tabbas ta saku ke nan, in kuwa ba ta shiga hannunta ba toh ba ta saku ba. Wannan shi ne ma’anar maganar mai Mukhtasar da yake cewa: والكتابة عازما, أو لا إن وصل لها.

3. A gurin Shafi’iyyah wanda duk ya rubuta cewa ya saki matarsa, in har ya yi niyyar sakinta toh kuwa sakin ya auku ke nan, in kuwa bai yi niyyar sakinta ba toh sakin bai auku ba har sai ya hurta da harshensa tukun.

4. A gurin Hanbaliyyah wanda duk ya rubuta boroboro cewa ya saki matarsa toh tabbas sakin ya tabbata sawaa’un ya yi niyyar sakin ko kuwa bai yi niyyar sakin ba, toh amma in ya rubuta sakin ne kawai domin ya tsoratar da matar, ko kuwa domin wani abu mai kama da haka, toh sakin bai auku ba.

5. A gurin Zahiriyyah sakin mace ba ya tabbata ta hanyar rubutu kawai, dole ne sai in an hada da hurucin harshe, matukar ba hurucin harshe ga wanda ke da ikon huruci toh kuwa ba saki ke nan.

6. Ni a nan ina ganin mazhabar Zahiriyyah tana da kyau sosai; saboda haka na zabe ta.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *