1. Sahabban da suka ciyar suka yi yaki kafin fathu Makka, da wadanda suka ciyar suka yi yaki bayan fathu Makka, dukkansu Allah Ya yi musu alkawarin Aljanna, duk da yake na farkon sun fi na bayan girman daraja a gurin Allah.

2. Allah Ya ce cikin suratul Hadid aya ta goma:-
لا يستوي منكم من أنفق من قبل الفتح وقاتل أولئك أعظم درجة من الذين أنفقوا من بعد وقاتلوا وكلا وعد الله الحسنى.
((Wadanda daga cikinku suka ciyar suka yi yaki kafin fathu Makka ba daidai suke da wadanda suka ciyar suka yi yaki bayan fathu Makka ba, lalle wadancan sun fi girman daraja, amma ko wanne daga cikinku Allah Ya yi masa alkawarin Aljanna)).

3. Allah muke rokon Ya kara wa Sahabbai yarda; Muhajiransu, da Ansarawansu, Ahlul Baiti daga cikinsu, da wadanda suke ba Ahlul Baiti ba. Ameen.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *