1. Yin budabaki daga tabbatar faduwar Rana sunna ce ta Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, sannan rashin yin haka da sunan Addini bidi’a ce mummuna.

2. Dare na farawa ne da zarar Rana ta fadi; wannan shi ne abin da Dictionaries na Larabci suka tabbatar, shi ne kuma abin da hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah suka tabbatar, shi ne kuma da yawa daga cikin littafan ‘yan shi’a rafidha su ma suka tabbatar.

3. Ya zo cikin Al-Qamusul Mueet kamar haka: الليل من مغرب الشمس ((Dare daga faduwar Rana ne)). Ya kuma zo cikin Lisaanul Arab kamar haka: الليل عقيب النهار ومبدؤه من غروب الشمس ((Dare na zuwa ne karshen Yini, kuma farkonsa na farawa ne daga faduwar Rana)). Wannan shi ne abin da littafan harshen Larabci suka tabbatar.

4. Ya zo cikin Buhari hadithi na 1,954, da Muslim hadithi na 1,100 daga Umar Bin Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: اذا اقبل الليل من ههنا وأدبر النهار من ههنا وغربت الشمس فقد أفطر الصائم ((Idan Dare ya fiskanto ta nan, kuma Yini ya ba da baya ta nan, tabbas mai azumi ya kare azuminsa)). Har yanzu Buhari ya ruwaito hadithi na 1,957, da Tirmiziy na 699, da Nasaa’iy na 3,298, da Ibnu Majah na 1,697, daga Sahl Bin Sa’ad Allah Ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: لا يزال الناس بخير ما عجلوا الفطر ((Mutane ba za su gushe cikin alheri ba matukar suna gaggauta budabaki)).

5. Littafan shi’a ma sun tabbatar da cewa da zarar Rana ta fadi to azumin mai azumi ya kare ke nan. Ashaikhus Saduq ya ce cikin littafin Man Laa Yahduruhul Faqeeh 2/129:  روى عمرو بن شمر عن إبي جعفر عليه السلام قال قال رسول الله صلى الله عليه واله: إذا غاب القرص أفطر الصائم ودخل وقت الصلاة ((Amr Bin Shimr ya ruwaito daga Abu Ja’afar alaihis Salam ya ce Manzon Allah mai tsira tare da iyalansa ya ce: Idan kwayar Rana ta bace mai azumi ya kare azuminsa ke nan, kuma lokacin Salla ya shigo)). Irin wadannan hadithai a littattafan shi’a suna da yawa.

6. Ke nan da Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: ثم أتموا الصيام إلى الليل ((Sannan sai ku cika azumi zuwa dare)) yana nufin zuwa faduwar Rana ne ba wai zuwa bayyanar Taurari ba. Allah Ya tabbatar da mu a kan Sunna, Ya kuma raba mu da bidi’a. Ameen

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *