Yana da kyau al’ummar Musulmi su san cewa ba dukkan wadanda Shi’ah Rafidha suka nada a matsayin limamansu ma’asumai ba suka amince da wannan bakar bidi’a tasu ta zagin sahabban Manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da kafirta su; misali a nan Babban Tabi’i Imam Ja’afarus Sadiq Allah Ya yi masa rahama, shi wannan ya kasance mai kin Shi’ah Rafidha ne, mai kuma kin wannan muguwar bidi’a tasu ne ta kafirta sahabban Manzon Allah mai tsira da aminci.
Imamuz Zahbiy ya yi tarjamar Imam Ja’afarus Sadiq cikin Siyar dinsa 6/ 362 ya ce: –
(( جعفر بن محمد بن علي بن الشهيد ابي عبد الله ريحانة النبي صلى الله عليه وسلم ومحبوبه الحسين بن امير المؤمنين ابي الحسن علي بن ابي طالب عبد مناف بن شيبة وهو عبد المطلب بن هاشم، واسمه عمرو بن عبد مناف بن قصي الامام الصادق شيخ بني هاشم ابو عبد الله القرشي الهاشمي العلوي النبوي المدني احد الاعلام، وامه هي ام فروة بنت القاسم بن محمد بن ابي بكر التيمي، وامها هي اسماء بنت عبد الرحمن بن ابي بكر ولهذا كان يقول: ولدني ابو بكر الصديق مرتين، وكان يغضب من الرافضة ويمقتهم اذا علم انهم يتعرضون لجده ابي بكر ظاهرا وباطنا، هذا لا ريب فيه، ولكن الرافضة قوم جهلة قد هوى بهم الهوى في الهاوية، فبعدا لهم))
Ma’na: (( Ja’afar Dan Muhammad Dan Aliyyu Dan Shahidi Abu Abdillah abin kaunar Annabi mai tsira da aminci kuma jikansa kuma masoyinsa Husain Dan Amirul Muminina Abul Hasan Aliyyu Dan Abu Talib Abdu Manaf Dan Shaibah wanda shi ne Abdulmuttalib Dan Hashim, sunansa shi ne Amr Dan Abdu Manaf Dan Qusai Al-Imamus Sadiq shugaban dangin Banu Hashim Abu Abdillah Baquraishe Ba’alawe Jinin annabta, Dan Madina, Daya daga cikin Shugabanni. Uwarsa kuwa ita ce Farwah Bint Al-Qasim Dan Muhammad Dan Abubakar At-Taimiy, uwarta kuwa ita ce Asmaa Bint Abdirrahman Dan Abubakar, wannan ya sa yake cewa: Abubakar As-Siddiq ya haife ni har sau biyu. Kuma ya kasance yana hushi da Rafidhawa, yana kuma kushe musu idan ya san cewa suna zagin kakansa Abubakar a bayyane ko a boye. Wannan babu shakka cikinsa sai dai Rafidhawa wasu mutane ne jahilai da son zuciya ya dulmuya su cikin Hawiyah, tir da su)).
Your article helped me a lot, is there any more related content? Thanks!