SHIFIDA:
1. Bayan mutuwar Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi tare da iyalansa, Quraishawa sun mulki duniyar Musulmi na tsawon shekaru 646, watau daga shekarar hijira ta 11 har zuwa shekarar hijira ta 656, wanda ya yi daidai da shekarar miladiyyah ta 632 har zuwa shekarar miladiyyah ta 1258.
2. A cikin wadannan shekaru 646, Banu Taim بنو تيم sun yi mulkin shekara biyu da watanni uku a karkashin Khilafar Sayyidina Abubakr As-Siddiq ابو بكر الصديق عبد الله بن ابي قحافة عثمان بن عامر التيمي القرشي
3. Daga nan sai Banu Adiyy بنو عدي suka yi mulki na tsawon shekara 10 da rabi, a karkashin Khilafar Sayyidina Umar Bin Khattab أبو حفص عمر بن الخطاب العدوي القرشي.
4. Daga nan sai Banu Umayyah suka yi mulkin na tsawon shekaru 103, Sayyidina Uthman Bin Affan عثمان بن عفان بن أبي العاص بن أمية القرشي Khalifan Annabi na uku shi ne cikin Banu Umayyah ya fara yin mulki, ya yi kuma mulki har na tsawon shekara 12, sannan sai Sayyidina Mu’awiyah da kuma dansa da jikansa, sai kuma Sahabi Marwan Bin Hakam da dansa da kuma jikokinsa su wadannan sun yi mulki na tsawon shekaru 91 ne.
5. Daga nan kuma sai Banu Hashim بنو هاشم wadanda su kuma suka yi mulki na har na tsawon shekaru 528 da wata tara. Wanda ya fara mulki cikin Banu Hashim shi ne Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib أبو الحسن علي بن ابي طالب الهاشمي القرشي Khalifan Annabi na hudu, ya yi kuma mulki ne na tsawon shelara 4 da wata tara, daga nan sai dansa Sayyidina Hasan Bin Ali, wanda ya yi mulki na kusan watanni 7. Sai kuma Abdullahis Saffah أبو العباس عبد الله السفاح بن محمد بن علي بن عبد الله بن العباس بن عبد المطلب الهاشمي القرشي da kuma yayansa Abu Ja’afaril Mansur أبو جعفر المنصور عبد الله بن محمد بن علي بن عبد الله بن العباس بن عبد المطلب الهاشمي da kuma ‘ya’ya da jikokin shi Abu Ja’afaril Mansur.
6. Yana da kyau a lura da cewa su Banu Hashim sun yi mulki na hakika ne kawai na tsawon shekaru 118 da wata 9; watau daga shekarar hijirah ta 132 zuwa shekarar hijirah ta 246, sai kuma shekaru 4 da wata 9 na Khilafar Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib Allah Ya kara masa yarda, toh amma shekaru 410 da suka rage kusan mulkin suna ne kawai suka yi; watau za a nada khalifah ba’abbase bahashime a suna, amma kuma a bisa hakika masu mulkin su ne sojoji Turkawa da kuma ministoci Turkawa na ita Darular.
7. Sannan yana da kyau a san cewa: Bayan Banu Hashim sun karbi jagorancin duniyar Musulmi daga hannun Banu Umayyah, su Banu Umayyan sun ci gaba da yin mulki a Turai a yankin Andulus الأندلس Andalucia/Andalusia, har zuwa lokacin da Granada غرطانة ta fada hannun sarakunan Turawa Kiristoci tukun a shekarar hijirah ta 897, wacce ta yi daidai da shekarar miladiyyah 1492.
JAUHARIN SAKONMU:
1. Saboda tarin wauta da tarin bidi’ah na Rafidhawa sai suka kasance suna kafirta Khalifah Abubakarus Siddiq daga Banu Taimin. Suka kasance suna kafirta Khalifah Umar Bin Khattab daga Banu Adiyyin. Suka kasance suna kafirta dukkan Khalifofin da suka yi mulki daga Banu Umayyah, kama daga Khalifah Uthman Bin Affan, da Khalifah Mu’awiyah Bin Abi Sufyan har zuwa na karshensu. Suka kasance suna kafirta kusan dukkan Khalifofin Banu Hashim, in banda Sayyidna Aliyu da Sayyidina Hasan, da wasu kadan daga Banul Abbas!!
2. San har yanzu su Rafidhawa sun kasance suna kafirce wa dukkan littattafan hadithi na Ahlus Sunnah; saboda suna daukan wadanda suka ruwaito hadithan littattafan Ahlus Sunnah mutane ne makaryata. Haka nan suna daukan dukkan Khalifofin Banu Umayyah kafurai ne makaryata kuma la’anannu!
3. Toh amma kuma a dukkan Duniya ana sane da cewa Banu Umayyah ne a karkashin Khalifah Uthman Bin Affan suka tara suka kuma rubuta Alkur’anin da dukkan Duniya suke karantawa tun daga zamanin shi Sayyidina Uthman har zuwa wannan zamani namu!
4. Abin da ya faru shi ne: Shi Sayyidina Uthman ya nada kwamiti ne da ya hada da Zaid Bin Thabit زيد بن ثابت da Abdullah Bin Zubair عبد الله بن الزبير da Sa’id Bin Ass سعيد بن العاص da Abdurrahman Bin Harith عبد الرحمن بن الحارث ya sa membobin kwamitin suka tattara Alkur’anin da yake hannunmu yanzu, ya sa su suka rubuta kwafe hudu, ko kuwa kwafe biyar, ko kuwa kwafe shida, ko kuwa kwafe bakwai, ko kuwa kwafe takwas. Ya rike kwafe daya a gurinsa a Madinah, sannan ya tura kwafe daya zuwa Makka, kwafe daya zuwa Kufah, kwafe daya zuwa Basrah, kwafe daya zuwa Damashq, kwafe daya zuwa Yaman, kwafe daya zuwa Masar, kwafe daya zuwa Bahrain.
5. Don Allah in banda bakar wauta, da bakar kidimar bidi’ah irin ta Rafidhawa ba, ta kaka ne za ku kafirta mutane, ku karyata su, ku la’ance su, sannan kuma ku dawo ku amince da Alkur’anin da su ne suka tattara shi, suka rubuta shi, suka ruwaito muku shi? Haka nan in banda shirme irin na Rafidhawa ba ta kaka ne za ku karbi ruwayar Alkur’ani da mutane suka ruwaito muku, sannan kuma ku ki karbar ruwayar hadithi da su mutanen suka ruwaito muku? Ai a dai hankalce idan har mutanen ba su yi muku karya ba a cikin ruwayar Alkur’ani da suka yi muku, toh kuwa ba za su yi muku karya ba a cikin ruwayar Hadithin da za su yi muku; wannan dai shi ne abin da masu hankali za su fahimta. Haka nan idan har su mutanen nan za su iya muku karya cikin ruwayar Hadithi saboda kafircinsu da rashin amanarsu, toh kuwa lalle a dai hankalce su wadannan mutanen tabbas za su iya muku wannan karyar cikin ruwaito muku Alkur’ani ma saboda dai wannan kafirci nasu da kuma rashin amanar tasu.
6. A hankalce abin da zai lazimci Rafidhawa shi ne dayan abu biyu: Ko dai su kafirce wa Alkur’anin da yake hannayensu yanzu; saboda Alkur’ani ne da Banu Umayyah wadanda suke kafurai ne la’anannu suka tattara, suka rubuta, suka ruwaito wa Duniya! Ko kuma su tuba zuwa ga Allah su dawo su karbi ingantattun hadithan da Ahlus Sunnah suka ruwaito wa Duniya; Ahlus Sunnan nan da suke dauka a matsayin kafurai la’anannun karnukan farautar Banu Umayyah!