1. Babban jigon akidar Shi’ah shi ne: Ismar Shugabanni; ma’anar hakan shi ne: Shugabanninsu da suka nada mutum 12 ba sa yin zunubi; manyan zunubai da kananansu, haka nan ba sa mantuwa, haka nan ba sa kure bisa ganganci ko bisa rabkanuwa!!

2. Wadannan mutum 12 da suka nada wa kansu, kuma suka ba su irin wannan matsayi da ya saba wa Shari’ar Musulunci, ya saba wa waki’in wadannan mutanen da suka nada, ga sunayensu kamar haka: Aliyyu Bin Abi Talib, Hasan Bin Aliy, Husain Bin Aliy, Zainul A’abideen, Muhammadul Baqir, Ja’afarus Sadiq, Musal Kaazim, Aliyyur Ridhaa, Muhammadul Jawad, Aliyyul Haadiy, Hasanul Askariy, Muhammadul Mahdiy.

3. Tabbas abin da Shari’ar Musulunci ta zo mana shi shi ne: Dukkan mutane suna yin kure, Annabinmu Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ya yi rabkanuwa a cikin salla har sau biyar, sannan kuma ya ce yana yin mantuwa kamar yadda mutane suke yin mantuwa, kuma Allah Ubangijinsa ya ce da shi: Ya gafarta masa zunubansa da ya aikata da can da kuma wadanda zai aikata a nan gaba.

4. Sannan dukkan mai karanta littattafan Hadithi, da littattafan Tarihi zai ga inda Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib Allah Ya kara masa yarda ya yi kurakurai da yawa. Sannan ya zo cikin littafin Shi’ah Al-Kafiy 8/356, da Nahjul  Balagah 2/201 cewa shi Sayyidina Aliyyu ya yi wa jama’arsa jawabi a cikin jawabin ya ce:
((فإني لست في نفسي بفوق أن أخطئ ولا ءامن ذلك من فعلي إلا أن يكفي الله من نفسي)).
Ma’ana: ((Ni game da kaina ban wuce in yi kure ba, kuma ba ni da garatin rashin kure cikin aikina sai in Allah ya tsare mini)).

5. Ke nan wannan babban jigo nasu “Ismar Shugabanni goma sha biyu” tsabar karya ce da rudu da ya saba wa abin da Shari’ar Musulunci ta zo da shi. Lazimin wannan shi ne kasancewar Shi’anci Rafidhanci tsantsar rudu da karya tun daga tushensa.

107 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *