1. A duk Duniyan nan babu wanda ya isa cikin ‘yan Shi’ah Rafidha ya kawo wa Duniya wani nassi sahihi sarihi a kan imamar Sayyidina Aliyyu ga duniyar Musulmi bayan mutuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
2. Abu na farko shi ne: Yana da kyau a san cewa Nassi mafi shahara da Rafidhawa suke kafa hujja da shi a kan Wisayar Imamah ga Aliyyu Bin Abi Talib shi ne hadithin Ghadir Khumm “Man kuntu maulaahu fa Aliyyun maulaah” من كنت مولاه فعلي مولاه shi kuwa wannan Hadithi ba nassi ba ne bayyananne watau ba nassi ba ne sarihi a kan ita Imamar Sayyidina Alin.
3. A nan wani zai iya cewa: Wane ne ya ce من كنت مولاه فعلي مولاه ba nassi ba ne Sarihi a kan Imamar Aliy? Amsa a nan ita ce: Akwai manyan malamai ma daga Rafidhawa da suka sam ba nassi ba ne sarihi a kan imamar Aliyyu cikinsu kuwa akwai Ash-Shariful Murtadhaa wanda ya mutu a shekarar hijirah ta 436, الشريف المرتضى علي بن الحسن الموسوي ya ce cikin littafinsa mai suna Rasaa’ilul Murtadhaa 1/338-339:-
((إن النص على ضربين: موسوم بالجلي، وموصوف بالخفي، وأما الجلي فهو الذي يستفاد من لفظه النص بالإمامة، كقوله عليه السلام: “هذا خليفتي من بعدي”، و”سلموا على علي عليه السلام بإمرة المؤمنين”• وليس معنى الجلي أن المراد منه معلوم ضرورة، بل ما فسرناه. وهذا الذي سميناه “الجلي” يمكن دخول الشبهة في المراد منه وإن بعدت، فيعتقد معتقد أنه أراد “بخليفتي من بعدي” بعد عثمان، ولم يرد بعد الوفاة بلا فصل. وأما النص الخفي فهو الذي ليس في صريحة لفظه النص بالإمامة وإنما ذلك في فحواه ومعناه، كبر الغدير، وخبر تبوك)).
Abin da ya ce cikin wannan Larabci a takaice shi ne: Hadithin Ghadir Khumm ba nassi ba ne sarihi a kan Imamar Aliy. Ya ce: Misalin nassi sarihi shi ne Annabi ya ce: “Wannan shi ne khalifana a bayana” ko ya ce: “Ku yi wa Aliyyu alaihis salam gaisuwar sarautar Muminai”. Sannan akwai wani malamin ma na biyu, wannan kuwa shi ne: Alaa’ud Deen Aliy Bin Hassan Al-Halabiy wanda ya mutu a karni na shida na hijirah علاء الدين علي بن الحسن الحلبي shi kuma ya ce cikin littafinsa mai suna: Khilaafatul Imami Aliy shafi na 52 خلافة الإمام علي بن ابي طالب عليه السلام بالنص ام بالنصب؟ :-
((إن حديث غدير خم من الأحاديث المحتملة للتأويل، ومنها الخفية المحتملة للتأويل، أولها نص يوم الغدير قوله صلى الله عليه وءاله: ((من كنت مولاه فعلي مولاه”))
Abin da ya ce a takaice shi ne: Hadithin Ghadir nassi ne boyayye da zai dauki tawiloli.
4. Abu na biyu da ya kamata a sani shi ne: Nassi da Tarihi a gurin Ahlus Sunnah da Rafidhawa duka sun tabbatar da cewa kwana uku kafin Annabi mai tsira da amincin Allah ya rasu, Bappansa Abbas Bin Abdilmuttalib ya ce wa Aliyyu Bin Abi Talib ina ganin Annabi ya yi kusan mutuwa; domin ina gane alamar mutuwa daga fiskokin zuriyar Abdulmuttalib, kuma ni ina ganin bayan kwana uku daga yanzu za ka zamanto ne cikin masu karban umurni kawai; saboda haka ka zo mu je gurin Manzon Allah mu tambaye shi: Shin wane ne Al’amarin nan (mulkin duniyar Musulmi) zai kasance a hannunsa? Idan a hannunmu ne (mu Banu Abdilmuttalib) sai mu sani, in kuma a hannun wasunmu ne sai mu umurce shi ya yi wasiyyarsa (watau ita Khilafar) zuwa gare mu. Sai Aliyyu Bin Abi Talib ya ce da shi: Wallahi in har muka roki Manzon Allah Khilafar sannan ya hana mu ita toh ina ganin har abada mutane ma ba za su ba mu ita ba; saboda haka ni dai har abada ba zan roki Manzon Allah ita ba.
Ga yadda nassin kissar ya zo a cikin Sahihul Bukhariy hadithi na 6,266, da kuma cikin Musnad na Imam Ahmad hadithi na 2,374:-
((عن ابن عباس رضي الله عنه ان علي بن ابي طالب رضي الله عنه خرج من عند النبي صلى الله عليه وسلم في وجعه الذي توفي فيه، فقال الناس: يا أبا الحسن كيف أصبح رسول الله صلى الله عليه وسلم? قال: أصبح بحمدالله بارئا. فأخذ بيده العباس فقال: ألا تراه؛ أنت والله بعد الثلاث عبد العصا، والله إني لأرى رسول الله صلى الله عليه وسلم سيتوفى في وجعه، وإني لأعرف في وجوه بني عبد المطلب الموت، فأذهب بنا إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فنسأله فيمن يكون الأمر ؟ فإن كان فينا علمنا ذلك، وان كان في غيرنا أمرناه فأوصى بنا. قال علي: والله لئن سألناها رسول الله صلى الله عليه وسلم فيمنعنا لا يعطيناها الناس ابدا، وإني لا أسألها رسول الله صلى الله عليه وسلم أبدًا)).
Sannan ga yadda nassin kissar ya zo a cikin littattafan Rafidhawa, a cikin littafin الفصول المختارة من العيون والمحاسن a shafi na 252, talifin babban malamin Rafidhawa الشريف المرتضى علي بن الحسن الموسوي wanda ya mutu a shekarar hijirah ta 436:-
((فصل: وقد سأل المخالفون في شيء يتعلق بهذا الفصل عن سؤال لم أجد لأحد من أصحابنا فيه جوابا، فأجبت عنه بما أسقطه على البيان، وهو أن قالوا: إذا زعمتم أن النبي ص قد نص على أمير المؤمنين عليه السلام بالإمامة وبين عن فرض طاعته، ودعا الأمة إلى اتباعه فما معنى قول العباس بن عبد المطلب رحمة الله عليه لأمير المؤمنين في مرض رسول الله ص: با ابن أخي ادخل معي إلى النبي ص فأسأله عن الأمر من بعده هل هو فينا فتطمئن قلوبنا أم هو في غيرنا فيوصيه لنا؟ فدخلا عليه فسأله العباس عن ذلك فلم يجبه هل هو فيهم او في غيرهم. فقال لهم: على رسلكم معشر بني هاشم أنتم المظلومون بني أنتم المقهورون)).
5. Kamar yadda kuke gani a ruwayar Ahlus Sunnah Aliyyu yaki su je su tambayi Annabi cewa wane ne zai zama Khalifan Musulmi idan shi Annabi ya mutu, amma a ruwayar Afidhawa Aliyyu da Abbas din sun je gurin Annabin kuma Abbas ya tambaye shi Annabi: wane ne zai zama Khalifan Musulmi bayan mutuwarsa? Toh sai dai shi Annabi mai tsira da amincin Allah ya ki ya ba su amsa, illa dai ya ce da su za a zalunce su kuma za a rinjaye su!!
6. Babban abin da wannan ingantacciyar Kissar take nuna wa Duniya shi ne: ikirarin da Rafidhawa suke yi na cewa Manzon Allah ya nada Sayyidina Wliyyu a matsayin khalifan al’ummar musulmin Duniya bayan mutuwarsa a hudubarsa da ya yi a Ghadir Khumm karya ce kawai; domin shi kansa Aliy bai san da wannan Hakikar ba, haka nan Bappansa Abbas Bin Abdilmuttalib shi mai bai san wannan Hakikar ba; domin kuwa da sun san da wannan Hakikar ta cewa: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi wasiyyar Khilafah a Ghadir Khumm toh da ba su yi shawarar su je su tambayi Annabi ba a kan cewa wane ne zai zama Khalifansa bayan mutuwarsa.
Thank you for your sharing. I am worried that I lack creative ideas. It is your article that makes me full of hope. Thank you. But, I have a question, can you help me?
Thanks for sharing. I read many of your blog posts, cool, your blog is very good.
Thanks for sharing. I read many of your blog posts, cool, your blog is very good.