1. Abin da ya tabbata cikin Sunnah Taqririyyah ta Manzon Allah mai tsira da amincin Allah shi ne bayyanar da fikon Sahabbai uku kadai; watau Sayyidina Abubakar, sai kuma Sayyidina Umar, sai kuma Sayyidina Uthman. Ni a iya sanina banda wadannan Sahabbai guda uku, babu kuma wani Sahabi daga cikin Sahabbai: Muhajirai da Ansar, Ahlul Baiti da wasun Ahlul Baiti da wani nassin Sunnah ya yi nassi a kan cewa shi din nan shi ne na hadu a daraja, ko shi ne na uku, ko shi ne na biyu, ko shi ne na farko, ko shi ne na kaza da kaza a daraja.

2. Ga Hadithai na taqriri da suka yi nassi a kan cewa Sayyidina Abubakar shi ne na daya a daraja a idanun Shari’ar Musulunci, sai kuma Sayyidina Umar shi ne na biyu, sai kuma Sayyidina Uthman shi ne na uku. Daga nan ba a ambaci kowa ba a matsayin na hudu, ko na biyar, ko na wani abu mai kama da haka:-


روى البخاري: ٣٦٩٧، وأبو داود:٤٦٢٧ عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: ((كنا في زمن النبي صلى الله عليه وسلم لا نعدل بأبي بكر احدا، ثم عمر، ثم عثمان، ثم نترك أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم لا نفاضل بينهم)).
Bukhariy ya ruwaito a hadithi na 3,697, da Abu Dawud na 4,627 daga Abdullahi Bin Umar Allah Ya kara musu yarda ya ce: ((Mun kasance a zamanin Annabi mai tsira da amincin Allah ba ma daidaita kowa da Abubakar, sannan sai Umar, sannan sai Uthman, sannan sai mu bar Sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah ba ma fifita tsakaninsu)).
وروى أبو داود:٤٦٢٨ بسند صحيح عن ابن عمر قال: ((كنا نقول ورسول الله صلى الله عليه وسلم حي: أفضل أمة النبي صلى الله عليه وسلم بعده أبو بكر، ثم عمر، ثم عثمان رضي الله عنهم أجمعين)).
Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 4,628 da isnadi sahihi daga Abdullah Bin Umar ya ce: ((Mun kasance muna cewa alhalin Annabi mai tsira da amincin Allah yana raye: Mafi darajar al’ummar Annabi mai tsira da amincin Allah bayan shi Annabin shi ne Abubakar, sai kuma Umar, sai kuma Uthman Allah Ya kara yarda da su dukkansu)).
وروى ابن ابي عاصم في السنة:١١٩٣ بسند صححه الالباني في تخريج كتاب السنة رقم:١١٩٦ عن ابن عمر رضي الله عنه قال: ((كنا نتحدث على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم أن خير هذه الأمة بعد نبيها ابو بكر، ثم عمر، ثم عثمان، فيبلغ ذلك النبي صلى الله عليه وسلم فلا ينكره)).
Abubakar Bin Abi A’asim ya ruwaito cikin littafin Sunnah hadithi na1,193 da isnadi sahihi kamar yadda Albaniy ya bayyana a cikin takhrijinsa ga littafin, daga Abdullah Bin Umar ya ce: ((Mun kasance muna cewa a zamanin Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi: Lalle mafi darajar wannan Al’ummah bayan Annabinta shi ne Abubakar, sai kuma Umar, sai kuma  Uthman, kuma labarin ya kai ga Annabi mai tsira da amincin Allah ba tare da ya yi musun hakan ba)).

3. Akwai Hadithin Sahabbai 10 da aka yi musu albishir da cewa su ‘yan Aljannah ne, aka kuma jera sunayensu kamar haka: Abubakar, Umar, Uthman, Aliyyu, Zubair Bin Awwam, Talhah Bin Ubaidillah, Abdurrahman Bin Auf, Sa’id Bin Zaid, Sa’ad Bin Abi Waqqas, Abu Ubaidah Bin Jarrah.


((أَبُو ‌بَكْرٍ ‌فِي ‌الجَنَّةِ، وَعُمَرُ فِي الجَنَّةِ، وَعُثْمَانُ فِي الجَنَّةِ، وَعَلِيٌّ فِي الجَنَّةِ، وَطَلْحَةُ فِي الجَنَّةِ وَالزُّبَيْرُ فِي الجَنَّةِ، وَعَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنُ عَوْفٍ فِي الجَنَّةِ، وَسَعْدٌ فِي الجَنَّةِ، وَسَعِيدٌ فِي الجَنَّةِ، وَأَبُو عُبَيْدَةَ بْنُ الجَرَّاحِ فِي الجَنَّةِ)).
Toh shi wannan tsarin jera sunayen ba ya nuna tartibinsu a daraja; saboda a ka’idar Larabci shi harafin wau و tarayya ce kawai yake nunawa ba wai tartibi ba. Wannan dai abu ne sananne a gurin masu karatun ilmin Nahwu.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *