Duk abin da yake ginshiki ne a akidar Shi’ah Rafidha toh za a tarar da cewa sam babu shi babu labarinsa a cikin Alkur’ani mai girma, sai dai a tarar da kishiyarsa.

Na daya: Yana daga cikin ginshikin addinsu Wajibcin wilayar mutane 12 da suka nada wa kansu, watau Aliyyu, Hasan, Husain, Aliyyu Zainul Abideen, Muhammadul Baqir, Ja’afarus Sadiq, Musal Kazeem, Aliyyur Rudhaa, Muhammadul Jawad, Aliyyul Hadiy, Hasanul Askariy, Muhammadul Mahdiy. Tabbas babu wannan Wilayar cikin Alkur’ani balle kuma wajibcinta, haka nan babu sunan ko da mutum guda ne cikin wadannan mutane 12 da suka nada wa kansu a cikin Alkur’ani mai girma. Toh amma Alhamdu Lillahi akwai kishiyar wannan Wilaya ta karya a cikin Alkur’ani mai girma, watau inda Allah yake cewa: Al’amarin al’ummar Musulmi Shura ne a tsakaninsu. Allah Ya ce a cikin suratush Shuraa aya ta 38:-
((والذين استجابوا لربهم وأقاموا الصلاة وأمرهم شورى بينهم ومما رزقناهم ينفقون)).

Na biyu: Yana daga cikin ginshikin addin Shi’ah Rafidha yin imani da Ismar khalifofi 12 da suka wajabta, watau dole ne kowa ya yi imani da cewa wadannan mutum 12 ba sa zunubi, ba sa mantuwa, ba sa kure!! Tabbas wani mutum mai irin wannan siffa a cikin Alkur’ani mai girma, ballantama a ce wajibi ne a yi imani da shi. Amma akwai kishiyar wannan ismah ta karya a cikin Alkur’ani mai girma, a inda Allah Madaukakin Sarki Ya tabbatar wa Duniya cewa hatta Manzon Allah mai tsira da amincin Allah shi ma ba yi da Ismah Mudlaqah, sai dai Ismah Muqayyadah wacce ta shafi isar da Manzancinsa ga al’ummar Duniya, ga abin da Allah Yake ce game da ManzonSa:-
((إنا فتحنا لك فتحا مبينا ليغفر لك الله ما تقدم من ذنبك وما تأخر ويتم نعمته عليك ويهديك صراطا مستقيما وينصرك الله نصرا عزيزا)). سورة الفتح: ١-٣.
((عفا الله عنك لم اذنت لهم حتى يتبين لك الذين صدقوا وتعلم الكاذبين)) سورة التوبة: ٤٣.
((ما كان لنبي ان يكون له أسرى حتى يثخن في الأرض تريدون عرض الدنيا والله يريد الآخرة والله عزيز حكيم لولا كتاب من الله سبق لمسكم فيما أخذتم عذاب عظيم)) سورة الأنفال ٦٧-٦٨.

Na uku: Yana daga cikin ginshikin addinin Shi’ah Rafidha yin imani da cewa: Bayan da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya mutu toh dukkan Sahabbansa sun yi ridda, dukkan Ansar sun yi ridda, kusan dukkan Muhajirun sun yi ridda in banda mutum kamar 3 ko 4! Watau kamar: Abu Zar Al-Ghifaariy, da Salmanul Farisiy, da Ammar Bin Yasir, da Miqdad Bin Amr. Ga ma irin abin da suke ruwaitowa a cikin littafinsu amintattu:-
((أخرج الشيخ المفيد في كتابه  الاختصاص بسنده: عن محمد بن الحسن الصفار عن محمد بن الحسين عن موسى بن سعدان عن عبد الله بن القاسم الحضرمي عن عمرو بن ثابت قال: سمعت أبا عبد الله عليه السلام يقول: إن النبي صلى الله عليه وآله لما قبض ارتد الناس على أعقابهم كفارا إلا ثلاثا: سلمان، والمقداد، وأبو ذر الغفاري…)).
Ta yaya Allah da Ya san boye da bayyane Ya gaya wa Duniya labarin cewa Ya yarda da mutane kuma Aljannah ita ce makomarsu, sannan kai ka zo ka ce labarin da Allah Ya bayar ya zama karya, wadannan mutane sun yi ridda makomarsu ta zan Wuta ba Aljannah ba? Wane ne zai yi irin wannan bahagon aiki da bahagon tunani in banda Shi’ah Rafidha? Ga dai abin da Allah Ya ce a cikin Alkur’aninSa mai girma game da Sahabban Manzon Allah Muhajiransu da Ansarawansu:-
((وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ)). سورة التوبة: ١٠٠.
((مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡـَٔهُۥ فَـَٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا)). سورة الفتح: ٢٩.
(( لَا يَسۡتَوِي مِنكُم مَّنۡ أَنفَقَ مِن قَبۡلِ ٱلۡفَتۡحِ وَقَٰتَلَۚ أُوْلَٰٓئِكَ أَعۡظَمُ دَرَجَةٗ مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَقَٰتَلُواْۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ)) الحديد: ١٠.
((وكذلك جعلناكم أمة وسطا لتكونوا شهداء على الناس وسكون الرسول عليكم شهيدا)) البقرة:١٤٣.
((كنتم خير أمة اخرجت للناس تأمرون بالمعروف وتنهون عن المنكر وتؤمنون بالله)) ءال عمران: ١١٠.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *