1. A cikin watan Zul Qa’adh a shekarar hijira ta shida, wanda ya yi daidai da watan March Azar shekarar miladiyyah ta 627, a gindin wata bishiyar magarya, a wani guri kusa da garin Makkah da ake kira Hudaibiyyah, a yanzu kuwa ake kiran da suna Ash-Shamisiy, Sahabban Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, Muhajirai da Ansarawa -cikinsu akwai Abubakar da Umar- tsakanin mutane 1300, zuwa mutane 1500, suka yi wa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah mubaya’ah a kan cewa idan har ya tabbata cewa Quraishawa sun kashe jakadan Manzon Allah Uthman Bin Affan toh kuwa lalle za su yaki Quraishawan Makkah har mutuwa ba tare da gudu ba.

2. Tabbas dukkan wadannan Sahabbai Allah Ya san abin da yake cikin zukatansu na kamalar Imani; wannan ne ma ya sa Shi Allah Madaukakin Sarki Ya gaya wa Duniya cewa Ya yarda da su; wanda kuma duk Allah Ya yi shelar yarda da shi toh har a bada ba Zai yi hushi da shi ba; wannan shi ne ma ya sa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya gaya wa Duniya cewa dukkan wadannan Sahabbai da suka yi masa wannan mubaya’ar a Hudaibiyyah ‘yan Aljannah ne.
روى ابو داود: ٤٦٥٣، والترمذي: ٣٨٦٠، وأحمد: ١٤٧٧٨، وابن حبان: ٤٨٠٢ بسند صحيح عن جابر بن عبد الله رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: ((لا يدخل النار أحد ممن بايع تحت الشجرة)).
Tarjama: ((Babu mai shiga Wuta ko da mutum daya ne daga cikin wadanda suka yi mubaya’ah a karkashin Bishiya)).

3. Allah Madaukakin Sarki Ya bayar da labarin wannan yarda da ya yi wa wadannan Sahabbai a cikin Suratul Fathi ayah ta 18, Ya ce:
(لقد رضي الله عن المؤمنين إذ يبايعونك تحت الشجرة فعلم ما في قلوبهم فأنزل السكينة عليهم وأثابهم فتحا قريبا)). الفتح: ١٨.
Tarjama: ((Hakika Allah Ya yarda da Muminan a lokacin da suke maka mubaya’ah a karkashin Bishiyar, Ya kuma san abin da yake cikin zukatansu, saboda haka Ya saukar da nitsuwa a kansu, Ya kuma yi musu sakayyar wani budi na kusa)).

4. Kuma domin Allah Madaukakin Sarki Ya kara nuna musu gata sai Ya ce wa Duniya: Duk wanda ya kasa cika alkawarin rashin gudu da ya dauka toh ya yi wa kansa ne, wanda kuma ya cika wannan alkawarin toh kuwa lalle Zai ba shi lada babba. Sai Ya ce a dai wannan Surah ta Fathu ayah ta 10:-
((إن الذين يبايعونك إنما يبايعون الله يد الله فوق أيديهم فمن نكث فإنما ينكث على نفسه ومن أوفى بما عاهد عليه الله فسيؤتيه أجرأ عظيما)) الفتح: ١٠.
Tarjama: ((Lalle wadannan da suke maka mubaya’ah Allah ne suke yi wa mubaya’ar; hanun Allah na kan hannayensu, wanda ya warware ya yi wa kansa, wanda ya cika akawarin da ya yi wa Allah toh kuwa da sannu Zai ba shi lada babba)).  A nan sai ku lura da kyau za ku ga cewa: saboda Shi Allah Ya riga Ya mayar da su ‘yan Aljannah gaba dayansu sam bai ambaci irin azaba ko horon da Zai yi wa wanda ya kasa cika alkawarinsa ba, toh amma sai Ya ce: wanda ya cika yana da wani irin babban lada.

5. Kamar yadda muka ambata a sama, wannan mubaya’ar ba a kan kome aka yi ta ba sai a kan rashin gudu kawai, ko a kan lazimtar yaki har samun nasara ko kuwa mutuwa, ba a yi ta a kan salla ko azumi ko hajji ko wani abu mai kama da haka ba, a’a, a kan dai rashin gudu kawai da lazimin hakan. Ga wadannan Hadithai biyu da suke tabbatar da hakan:-
روى البخاري: ٢٩٦٠، ومسلم: ١٨٦٠ عن سلمة بن الأكوع رضي الله عنه قال: بايعت النبي صلى الله عليه وسلم ثم عدلت الى ظل الشجرة، فلما خف الناس قال: يا ابن الاكوع ألا تبايع؟ قال: قلت: قد بايعت يا رسول الله. قال: وأيضا فبايعته الثانية. قلت له: يا أبا مسلم على أي شيء كنتم تبايعون يومئذ؟ قال: على الموت)). وروى مسلم:١٨٥٦ عن جابر بن عبد الله قال: كنا يوم الحديبية الفا واربعمائة، فبايعناه وعمر آخذ بيده تحت الشجرة وهي سمرة. وقال: بايعناه على أن لا نفر)).

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *