1. Ni ina ganin cewa masu bidi’ar Shi’ah Imamiyyah sam ba su yi nazarin nassoshin Alkur’ani mai girma ba kafin su kirkiri wannan bidi’ah tasu ta امامية اثنا عشرية Imamamiyyah Ithnaa Ishriyyah; saboda tabbas da sun yi nazarin nassoshin Alkur’ani mai girma to da ba su kirkiri wannan bidi’ar kamar yadda take a halin yanzu ba; saboda rashin alakarta da Alkur’ani mai girma kwatakwata; babu sunan ko daya daga cikin Limaman nan 12 da aka ambata a cikin Alkur’ani, babu ambaton siffofinsu, babu ambaton darajojinsu, babu ambaton ayyukan da za su yi.

2. Kamar yadda aka sani ne cewa su wadannan Shi’ah Rafidha Imamiyyah, sun nada wa kansu Imamai goma sha biyu ne, sannan suka ce: “Ko wane Imami tamkar Annabi yake, kuma wajibi ne ya zarce dukkan mutane cikin siffofin kamala; siffar jarunta da karamci da kamun kai da gaskiya da adalci, haka nan wajibi ne ya zarce dukkan mutane iya tsare tsare da hankali da hikima da kuma kyawun dabi’ah”.

3. To amma abin mamaki shi ne: jigon kalmar da suka zaba wa wannan bidi’ah tasu, watau “Imam” kalma ce da zatinta bai samu wata kima ba a cikin Alkur’ani mai girma; domin ana danganta kafurai da ita kamar yadda ake danganta muminai da ita; sabanin kalmar “annabci” ko kalmar “siddikanci” da makamantansu, su wadannan Alkur’ani mai girma bai taba siffanta kafurai da su ba. Amma kalmar “imam” ko “a’immah” Alkur’ani mai girma ya siffanta kafurai da kalmar, ga ma misali nan:
﴿ وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّةً يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ ۖ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ لَا يُنصَرُونَ﴾ سورة القصص: 41.
((وَإِن نَّكَثُوٓاْ أَيْمَٰنَهُم مِّنۢ بَعْدِ عَهْدِهِمْ وَطَعَنُواْ فِى دِينِكُمْ فَقَٰتِلُوٓاْ أَئِمَّةَ ٱلْكُفْرِ ۙ إِنَّهُمْ لَآ أَيْمَٰنَ لَهُمْ لَعَلَّهُمْ يَنتَهُونَ)). سورة التوبة:12.

4. Sannan Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci mukaman waliyyanSa a cikin Alkur’ani mai girma a cikin Suratun Nisa’i ayah ta 69 Ya ce:
((وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّ‍ۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَٰٓئِكَ رَفِيقٗا)).
Tarjama: ((Duk wadanda suka yi wa Allah da Manzo biyayya to wadannan suna tare wadanda Allah Ya yi musu ni’ima daga Annabawa da Siddikai da Shahidai da Salihai, ya yi kyau wadannan su kasance abokan zama)). Kamar yadda kuka gani a nan Ya ambaci martabar waliyyinsa hudu kawai: (1) Annabawa. (2) Siddikai. (3) Shahidai. (4) Salihai, kuma a nan ma dai “Imamai” ba su samu shiga ba; duk da kuwa cewa darajarsu a gurin ‘yan bidi’ar shi’ah tamkar ta Annabawa take, ko ma ta zarce!

5. Lalle ni ina ganin cewa mutanen nan da suka kirkiro wannan bidi’ah ta shi’ah imamiyyah da dai sun yi nazarin nassoshin Alkur’ani mai girma da kyau kafin su kirkire ta to da watakila ba su sanya mata suna: “Imamiyyah” ba.

    8 Comments

    1. Thank you for your sharing. I am worried that I lack creative ideas. It is your article that makes me full of hope. Thank you. But, I have a question, can you help me?

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *