Mafi yawan Malaman Musulunci sun tafi a kan haramta mulkin mace, amma akwai ‘yan kadan da suka halatta hakan.

Masu haramtawa sun dogara ne da umuumin fadar Amanzon Allah mai tsira da aminci cikin hadithin Abu Bakrah Allah Ya kara masa yarda: ((Mutanen da suka jibintar da mace al’amarinsu sam ba za su yi nasara ba)).  Manzon Allah mai tsira da aminci ya fadi hadithin ne a lokacin da ya samu labarin cewa Farisawa (Iraniyawa) sun nada ‘Yar  Kisraa a matsayin sarauniyar daularsu. Kuma ba a dauki lokaci mai tsawo ba daular tasu ta rushe ta fada hannun Musulmi.  Haka nan Sahabi Abu Bakrah ya kafa hujja da Hadithin ne domin ya nuna cewa Nana A’isha da ta jagorancin yakin Hamal ba za ta yi nasara a kan Sayyidina Aliyyu ba.

Toh amma Malaman da suke ganin halaccin mace ta yi mulki su suna ganin cewa: An khassase umuumin wannan Hadithin; watau Hadithin ya kasance yana magana ne kawai a kan wadancan shugabannin Farisawa da suka nada ‘Yar Kisraa a matsayin sarauniya. Kuma abin da ya khassase wannan umuumin shi ne Waaqi’i, watau Hissi; saboda mata da yawa ne suka mulki al’ummominsu kuma suka yi nasara, ko suka rabauta rabauta ta irin ta Shari’ah; kamar mutanen Sarauniyar Sabaa wacce Sarauniyarsu ta ja su zuwa ga shiga Musulunci a gurin Annabi Sulaiman.

Kuma har yanzu suka ce: Akwai manyan Sahabbai kamar su Talhah Bin Ubaidillah da Zubair Bin Awwam da ba sa ganin haramcin mace ta yi shugabanci; domin sun yarda da shugabancin Nana A’isha Allah Ya kara mata yarda a yakin Jamal.

Masu ganin halaccin mulkin mace har yanzu sun ce: Waaqi’i ko Hissi da ya khassase Umumuin Hadithin: لن يفلح قوم ولوا امرهم امراة bayan sautar sarauniyar Sabaa, akwai
1. Prime Minister Margaret Thatcher ta Britain daga 1979-1990.
2. Ellen Johnson Sirleaf ta kasar Liberia, daga 2006-2018.
3. Chancellor Angela Merkel ta Germany daga 2005-2021.
4. Cristina Fernandez ta Argentina daga 2007-2015.
5. Michelle Bachelet ta Chile daga 2006-2018.
6. Benazir Bhutto ta Pakistan daga 1988-1990, da kuma 1993-1996.
7. Indra Gandhi ta India daga 1966-1977, da kuma 1980-1984. Suka ce: dukkan wadannan mata mulkinsu bai zan sanadin rushewar daulolinsu ba kamar yadda abin ya faru a kasar Farisa.

22 Comments

  1. На сайте https://ideal-okna57.ru/ вы сможете заказать пластиковые окна, а также москитные сетки, которые создаются из качественных, уникальных материалов. Поэтому они не утратят внешнего вида длительное время. Важным моментом является то, что замеры происходят абсолютно бесплатно, а вызвать мастера вы сможете прямо сейчас. Для того чтобы определиться с выбором, необходимо изучить весь каталог. Доставка продукции происходит абсолютно бесплатно и строго на обозначенный адрес. У компании опыт работы в данной сфере – более 10 лет.

  2. На сайте https://raschitat-online.ru/ воспользуйтесь специальным инженерным калькулятором, который выполнит все необходимые расчеты. При этом появляется возможность осуществить все самые сложные расчеты. И самое главное, что все процессы простые, быстрые, безопасные. Пользоваться устройством можно абсолютно бесплатно и независимо от вашего местоположения. Калькулятором можно воспользоваться на любом устройстве, в том числе, ПК, смартфоне. Если хотите расширить функции или предложить идею по улучшению работы сервиса, то заполните обратную связь.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *