1. Aikin Liman ne shi kadansa ya daga muryarsa cikin sallarsa domin ya jiyar da mamu sautinsa, su san halin da yake ciki cikin sallarsa.

2. Amma idan sautin Liman  ba ya iya isa ga mamunsa saboda rashin lafiya, ko yawan mamun, to mustahabbi ne Ladani, ko wanin ladani ya daga muryarsa domin sanar da sauran mamu abin liman ke ciki.

3. To amma idan sautin liman yana kai wa ga mamu, to tabbas bidi’ah ce abar kyama a wannan lokacin Ladan ko wani mutum daban ya rika daga muryarsa domin sanar da mutane halin da Liman ke ciki.

4. Wajibi ne al’ummar Musulmi a duk inda suke su rika yin abin da yake daidai, kada su damu da maganar masu cewa: to ai ana yin tasmi’i a Masallacin Harami na Makkah da Madinah! Kada su damu da irin wannan magana ta jahilai; saboda kasancewar wani ya aikata bidi’ah a Masallacin Haram na Makkah, ko a Masallacin Haram na Madinah ba ya zama hujja a mahangar Shari’ar Musulunci.

5. Kasa hana bidi’ar tabilgi a Masallatai biyu kacal a dukkan fadin Kasar Saudiyyah da gwamnatin Saudiyyah ta yi tabbas abin takaici ne, muna kuma fatan za su gyara. Muna rokon Allah Ya taimake su a kan sauran kyawawan ayyukansu na yada Sunnah. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *