1. Sallar da Manzon Allah صلى الله عليه وءاله وسلم tare da Sahabbansa suka yi wa Najashiy tana tabbatar da halaccin yi wa duk musulmin da ya mutu a wata kasa sallar janaza, sawaa’un an yi masa sallar janaza a can inda ya mutun ko kuwa a’a ba a yi masa ba. Wanda kuma duk ya yi ikirarin cewa abin da ya sa Manzon Allah da Sahabbansa suka yi wa Najashiy salla shi ne saboda babu wanda ya yi masa sallar ne a can Habashan, to wannan dole ne a ce ya kawo wa Duniya tabbataccen dalili a kan hakan; ko dai daga Alkur’ani ko kuwa daga ingantaccen Hadithi. Kuma har abada babu wanda ya isa ya kawo irin wannan dalilin.

2. Amma abin da Malaman Mazhabar Hanbaliyyah suke ce cikin  المغني 2/383 da الشرح الكبير 2/355 da المبدع 2/260 da كشاف القناع 2/123 shi ne: Najashiy Sarkin Habasha ne da ya musulunta kuma Musuluncinsa ya fita fili, ke nan zai yi wuya matuka a ce babu mutum daya da ya bi shi wanda kuma zai yi masa salla bayan mutuwarsa”.

3. Hafiz Ibnu Hajar ya ce a cikin Fathul Baariy 3/188: ((Ban ga inda aka ce babu ko da mutum daya da ya yi masa salla a Habasha ba.

4. Sai dai kuma shi Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce game da shi Najashiy a cikin Maj’muu’ul Fataawaa 19/217, da kuma cikin Minhaajussunnah 5/112 : ((Mutane kadan ne suka karbi Musulunci tare da shi; wannan shi ne ma ya sa a lokacin da ya mutu babu wanda ya yi masa salla)).

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *