HARMUN NE TUFAR KO WANE NAMIJI TA WUCE IDON SAWU:

Wajibi ne dukkan Musulmi su san cewa yin aiki da ingantattun hadithan Annabi cikin Aqidah, da Ibadah, da Mu’amalah wajibi ne a kansu, kuma alheri ne a gare su Duniya da Lahira.

Tabbas Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce Isbalin tufafi yanga ce. Imamu Abu Dawuda ya ruwaito hadithi na 4086 da Imamun Nasaa’iy Hadithi na 9611, da Imam Ahmad Hadithi na 20655, da isnadi sahihi daga Sahabi Jabir Bin Sulaim Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((وارفع ازارك الى نصف الساق فان ابيت  فالى الكعبين واياك واسبال الازار فانها من المخيلة وان الله لا يحب المخيلة)).
Ma’ana: ((Ka dage zaninka zuwa tsakiyar kwabrinka, in ka ki to zuwa idon sawunka, ka nisanci isbalin tufa lalle shi daga yanga yake, kuma lalle Allah ba ya son yanga)).
Imamut Tabraaniy ya ruwaito Hadithi na 7909, da Imam Ahmad Hadithi na 17782 da isnadi sahihi daga Sahabi Abu Umaamah ya ce: ((بينما نحن مع رسول الله صلى الله عليه وسلم اذ لحقنا عمرو بن زرارة الأنصاري في حلة ازار ورداء قد أسبل فجعل النبي الله صلى الله عليه وسلم يأخذ بناحية ثوبه وبتواضع لله ويقول: اللهم عبدك ابن عبدك ابن امتك حتى سمعها عمرو بن زرارة فالتفت الى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا رسول الله أني احمش الساقين. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: يا عمرو بن زرارة ان الله  عز وجل قد أحسن كل شيء خلقه. يا عمرو بن زرارة ان الله لا يحب المسبلين. ثم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم بكفه تحت ركبة نفسه فقال:  يا عمرو بن زرارة: هذا موضع الإزار. ثم رفعها ثم وضعهاتحت ذلك فقال:  يا عمرو بن زرارة هذا موضع الإزار. ثم رفعها ثم وضعها تحت ذلك فقال: يا عمرو بن زرارة: هذا موضع الازار)). Ma’ana: ((Muna tare da manzon Allah Mai tsira da amincin Allah sai Amr Bin Zurarah Al-Ansariy ya riske mu cikin wasu tufafi biyu na jinsi daya Zani da Mayafi ya yi kuma isbali, sai Annabi Mai tsira da amincin Allah ya fara rike wani bangare na tufarsa yana kaskantar da kari ga Allah yana cewa: Ya Ubangijina bawanKa ne Dan bawanKa Dan baiwarKa, har dai Amr Bin Zurarah ya ji abin da yake cewa ya waigo zuwa ga Annabi Mai tsira da amincin Allah, ya ce: Ya manzon Allah ni mutum ne mai siraran kwabri. Sai manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Ya kai Amr Bin Zurarah lalle Allah Mabuwayi Ya kyautata dukkan wata halitta da Ya halitta. Ya kai Amr Bin Zurarah lalle Allah ba Ya son masu yin isbali. Sai manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi nuni da tafin hannunsa zuwa ga kasan guiwarsa sannan ya ce: Ya Amr Bin Zurarah wannan shi ne bigiren Izari, sannan ya sake daga tafin hannun ya kuma sanya shi kasan hakan sannan ya ce: Ya Amr Bin Zurarah wannan shi ne bigiren Izari. Sannan ya sake daga tafin hannun ya kuma sanya shi kasan hakan sannan ya ce: Ya Amr Bin Zurarah wannan shi ne bigiren Izari)).

Lalle babu wani musulmin kirki da zai san wadannan hadithai ingantattu sannan ya ci gaba da kiran mutane cewa su rika yin isbali matukar dai isbalin da suke yi ba saboda yanga ba ce suke yin sa! Saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya riga ya gama magana a hadithin farko inda ya ce: shi kansa zatin Isbalin yanga ce a mahangar Shari’ah. Sannan a Hadithi na biyu ya hana Amr Bin Zurarah yin Isbali ya kuma gaya masa cewa Allah lalle Allah ba Ya son masu Isbali; duk kuwa da cewa Amr ya gaya masa dalilin da ya da yake yin Isbali watau kwabrisa ne yake siriri wannan shi ya sa yake rufe shi dukkan shi ba wai saboda alfahari da yanga ba.
*********************
A nan akwai abubuwa guda biyu wadanda suka banbanta da juna, kuma Shari’a ta banbanta su cikin hukunci, wadannan abubuwa biyu kuwa su ne kamar haka:-
1. Wanda tufarsa ta yi kasa da idon sawu koda kuwa ba ta ja kasa ba, shi wannan hukuncinsa shi ne cancantar shiga wuta. Hujja a kan haka ita ce: Imamul Bukhari ya ruwaito cikin sahihinsa hadithi na 5450′ daga Sahabi Abu Huraira Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((ما اسفل من الكعبين من الازار ففي النار)).
Ma’ana: ((Abin da ya yi kasa da idanun sawu daga tufafi to yana cikin Wuta)).
2. Wanda kuma tufarsa ke jan kasa da niyyar yanga, shi wannan hukuncinsa shi ne Allah Madaukakin Sarki ba zai dube shi ba a Ranar Kiyama. Hujja a kan haka ita ce: Imamul Bukhari ya ruwaito Hadithi na 3465, da Imamu Muslim Hadithi na 2085 daga Sahabi Abdullahi Bin Umar cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((من جر ثوبه خيلاء لم ينظر الله اليه يوم القيامة)).
Ma’ana: ((Wanda duk tufarsa ta ja kasa saboda yanga Allah ba zai dube shi ba a Ranar Kiyamah)).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *