Nau’in mazan da suke iya jawo wa ƴan’uwansu mata haƙƙin ta’asibi a babin gado nau’i huɗu ne kacal, kuma su ne kamar haka:
- Ɗa.
- Ɗan ɗa, ko da kuwa abin ya yi ƙasa sosai.
- Ɗan’uwa shaƙiƙi, amma banda ɗansa ko jikokinsa.
- Ɗan’uwa li’abi, amma banda ɗansa ko jikokinsa.
Da mutum zai mutu sannan ya bar ƴaƴan wansa (yayansa) ko ƙaninsa maza da mata, toh da mazan ne kaɗai za su gaje shi banda matan. Toh amma da zai mutu ya bar jikokin ɗansa namiji maza da mata toh da dukkan mazan da kuma dukkan matan ne za su gaje shi a bisa ƙa’idar ko wane namiji yana da rabon mace biyu.