Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa’iqamatis Sunnah ƙarƙashin Jagorancin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa ta ziyarci Jam’iar ta datake ginawa na AS-SALAM domin duba yadda aikin Jami’ar ke gudana.
Tawagar Shugaban wanda ya samu rakiyar manyan Shugabannin Ƙungiyar na ƙasa da kuma Shugabannin ginin Jam’iar wanda suka haɗa da Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Dr. Kabiru Haruna Gombe, Professor Abdullahi Sale Pakistan, Professor Umar Labɗo, Dr. Abduƙadir Saleh Kazaure, Dr. Magaji F. Zarewa, Dr. Abubakar Abdussalam Baban Gwale, Alh. Abubakar Sahabo Magaji, Engr. Ashiru Baban Dede da sauran Shugabanni.
Shugaban ya yabawa wanda suka bada gudumawar su domin ganin cigaban wannan aiki, kamar irin su Senator Barau Jibrin Deputy Senate President wanda ya gina Focolty guda na koyarda sana’a wanda an kammala shi ahalin yanzu, kuma ya sake Alƙawarin gina wani Focultyn ba tare da bata lokaci ba, Shugaban ya sake yabawa sanannen ɗan kasuwan nan Alh. Auwalu Abdullahi Rano wanda akafi sani da A.A Rano shima bisaga ga mashahuriyar aiki da shima ya ɗauko na gina Babban Foculty da kuma Alƙawarin kammala ta kafun watan Nuwambar wannan shekara ta 2023.
Shugaban ya sake mika godiyar sa ga Shugaban Jam’iyar APC na ƙasa Alh. Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Gidauniyar sa ta Ganduje Foundation bisaga babban gudumawar su na katafariyar makaranta da suka bawa wannan Ƙungiya a garin Malam-madori da kuma wata makarantar katafariya daya sake baiwa Ƙungiyar a garin Takai dake Jihar Kano Wanda ake shirin danƙata ga Ƙungiyar bayan kammala aikin ta.
Ƙungiyar tana duba yiyuwar soma karatu a wannan Jam’iar kafun ƙarshen wannan shekara ta 2023 In shaa Allah.
Daga ƙarshe Shugaban yace ƙungiyar tana mika godiyarta ga dukkan wanda suka bada gudunmawa wajen wannan aiki, kama daga wanda suka bada dukiyoyin su da wanda suka bada fatun Layyar don ganin wannan aiki ta cigaba.
Rashid Yahya Numan
S.A Media to National Chairman council of Ulama’Jibwis Nigeria 🇳🇬 and GD.
I don’t think the title of your article matches the content lol. Just kidding, mainly because I had some doubts after reading the article.