ALLAH WADAREN MATSAYIN BIDEN:

1. Muna Allah wadai da matsayin da Shugaba Joe Biden na America ya dauka a kan zaluncin da Kasar Isra’ila take yi wa Falasdinawa yau kusan 75 ke nan, da kuma irin abin da ita Isra’ilan take musu a yanzu haka a yankin Gaza (Ghazzah) na hana wa jama’arsu wutar lantarki, da rusa musu gidanjensu, da hana su ruwan sha, da abinci tare da kashe da yawa daga cikinsu duk kuwa da cewa suna karkashin mamayar su Isra’ilawan ne!!

2. Turawan mulkin mallaka ne a karkashin jagorancin America suka kafa kasar Isra’ila ta yanzu a ranar 14/05/1948, yau shekaru 75 ke nan da suka wuce, sun kuma kafa Kasar Isra’ilan ne a cikin Kasar Palestine (Falasteen), sannan suka kwaso Yahudawa daga Africa da Asia da Europe da North America da South America da Australia suka zuba cikin wannan Kasa ta Falasteen suka kuma tuttula musu makamai da kudi, sannan suka halatta musu daukar Falatinawa tamkar wasu dabbobi da ba su da hakki irin ‘Yan Adam!!

3. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya albarkaci Falasdinawa da kasarsu, Ya kuma la’anci makiyansu da masu musguna musu a duk inda suke cikin Duniyan nan. Muna rokon Sa Madaukakin Sarki Ya gaggauta musu samun yancinsu da yancin kasarsu. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *