1. Farko dai yana da kyau kowa ya san cewa idin maulidin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah bidi’a ne, kuma yarda da hallacin Idin, da kuma yin Idin a aikace dukkansu saba wa Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ne.

2. Sam ba daidai ba ne a dauki dukkan musulmin da hatsarin kauyen Tudun Biri ya ritsa da su a matsayin mutane ne da suke yin bidi’ar Idin Maulidi, ko kuwa mutane ne da suka yarda da halaccin bidi’ar idin maulidi.

3. Hadithai sun inganta a kan cewa akwai nau’ukan mutane har fiye da 20 da suke shahidai ne a mahangar Musulunci kamar yadda Haafiz Bin Hajar ya ambata a cikin littafinsa Fathul Baariy 6/43-44.

4. Daga cikin mutanen da hadithai suka inganta a kan cewa su shahidai ne akwai: Wanda ya mutu a fagen daga domin daukaka kalmar Allah, da wanda wata annoba ta kashe, da wanda ciwon ciki ya kashe, da wanda ya mutu cikin ruwa, da wanda gobara ta kashe, da wanda gini ya rushe a kansa ya mutu, da matar da ta mutu a lokacin haifuwa, da wanda tarin fuka (Tuberculosis TB) ya kashe, da wanda ya fado daga kan dabba ya mutu, da wanda maciji ko kunama ta harbe shi ya mutu, da wanda ya mutu a lokacin da yake cikin Ribaa’di, da wanda ya mutu a lokacin da yake cikin halin bakunta, da wanda aka kashe a lokacin da yake kare dukiyarsa, da wanda aka kashe a lokacin da yake kare addininsa na Musulunci, da wanda aka kashe a lokacin da yake kare jininsa, da wanda aka kashe a lokacin da yake kare yalansa…

5. Sai a duba cikin wadannan da sahihan nassoshin hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah suka zo da labarin cewa shahidai ne su, in akwai wadanda aka kashe su a lokacin da suke yin bidi’ar maulidi a cikin su wadannan Hadithan toh shi ke nan sai a kira su su ma da sunan Shahidai, in kuma babu toh ba za a kira su da sunan Shahidai ba, sai dai a rika cewa wadanda aka kashe su a lokacin da suke bidi’ar idin Maulidi. Wannan shi ne abin da ya bayyana gare mu. Allah Shi ne Mafi sani

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *