1. Na ji har daga mutum biyu cikin maluman Sufaye daya bakadire daya kuma batijjane da suka fito fili suna gaya wa Duniya cewa Allah ba mai tausayi ba ne, ba a sifanta Allah da tausayi! Wannan magana tana daure mini kai kullum.

2. Ga ni na zo da kokon barana ina rokon masana harshen Larabci da Hausa a hade da su taimaka su yi mana bayanin yadda wannan mas’ala take, watau dalilin da zai sa a kore tausayi ga Allah Madaukakin Sarki; duk da yake wasu daga cikin sunayenSa a fahimtata suna nuni a kan cewa Shi Mai tausayi ne, toh amma ta yiwu saboda rashin sanina ga ma’anar tausayi ne cikin harshen Hausa ya sa nake ganin haka.

3. Tabbas muna sane da cewa daga cikin sunayen Allah kyawawa akwai: الرحيم akwai kuma الرفيق sannan a cikin Dictionaries na Larabci ana cewa: يقال في قلبه رحمة اذا كان فيه رقة وشفقة. ويقال ايضا: الحنان: الرحمة.ويقال ايضا: الحنة:رقة القلب.

4. Abokanmu Hausawa kuma masa’ana Larabci da Shari’ah su taimaka su yi mana bayani.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *