1. Mazhabar mafi yawan maluman Musulunci, kuma zance mafi inganci wanda kuma ya dace da ingantaccen hadithi shi ne: duk yarinya ko yaron da aka haifa ta hanyar zina toh Shari’ar Musulunci ba za ta danganta su da mahaifinsu ba, kuma sam ba za su ci gadon mahaifin nasu ba, shi ma kuma ba Sam ba zai ci gadonsu ba, ko da kuwa shi mahaifin ya yarda da cewa shi ne ya haife su.
Babbar hujja a kan haka ita ce hadithi na 2,265 da Abu Dawud ya ruwaito, na 2,746 da Ibnu Majah ya ruwaito, na 7,042 da Ahmad ya ruwaito da isnadi mai kyau daga Abdullah Bin Amr Bin A’as Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
((إنَّ النبيَّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ قضَى أنَّ كلَّ مُستلحَقٍ اسْتُلحِقَ بَعدَ أبيهِ الذي يُدْعى له ادَّعاهُ وَرَثَتُه فقضَى أنَّ كلَّ مَن كان مِن أَمَةٍ يملِكُها يومَ أصابَها، فقدْ لَحِقَ بمَنِ استلحَقَهُ، وليس له ممَّا قُسِّمَ قَبلَه مِنَ الميراثِ شيءٌ، وما أدْرَكَ مِن ميراثٍ لم يُقسَّمْ فلَهُ نصيبُه، ولا يُلْحَقُ إذا كان أبوه الذي يُدْعى له أنكَرَه، وإنْ كان مِن أَمَةٍ لم يملِكْها، أو مِن حُرَّةٍ عَاهَرَ بها، فإنَّه لا يُلْحَقُ، ولا يَرِثُ، وإنْ كان الذي يُدْعى له هو ادَّعاهُ، فهو وَلَدُ زَنْيَةٍ، مِن حُرَّةٍ كان أو أَمَةٍ)).
Ma’ana: ((Lalle Annabi mai tsira da aminci ya yi hukunci game da riskakke da aka riskar bayan mutuwar mahaifinsa da aka dangata shi da shi, kuma masu gadon mahaifin suka yi ikirarin shi. Sai (shi Annabi) ya yi hukuncin cewa: Duk dan da aka haifa da wata kuyanga wacce ubansa ya mallaka a ranar da ya sadu da ita, toh wannan tabbas ya riskanta zuwa ga wannan da ya riskantar da shi zuwa gare shi, toh amma ba yi da wani abu na gado da aka riga aka raba kafin zuwansa (a zamanin jahiliyya), toh amma abin da ya tarar na kayan gado (a zamanin Musulunci) wanda ba a raba ba yana da rabonsa (cikin wannan). Amma ba za a riskar da shi ba idan uban da ake danganta shi zuwa gare shi ya yi musun cewa shi ne ya haife shi.
Toh amma idan Dan ya kasance daga wata kuyangace da ba shi ya mallake ta ba, ko kuwa ya kasance daga wata mace ce mai yanci da ya yi zina da ita, toh wannan sam ba za a riskar da shi ba, kuma ba zai yi gado ba, ko da kuwa wannan da ake danganta shi zuwa gare shi ya yi ikirarin cewa dansa ne shi; saboda kasancewarsa dan zina, ko dai daga mace mai yanci ko kuwa daga kuyanga)).
2. Toh amma daga cikin Malamai Salaf da kuma Khalaf akwai ‘yan kadan da suke ganin cewa: Idan wani ya yi zina da mace kuma ta haifa masa yaro ko yarin’ya sannan ya amince da cewa dansa ne ko kuwa ‘yarsa ce, toh tabbas Shari’ar Musulunci ta riskar masa da abin da ya riskar ma kansa; saboda haka wadannan yaran za su gaje shi, shi ma kuma zai gaje su. Wannan maganar ita ce mazhabar Urwah Bin Zubair, da Sulaiman Bin Yasar, da Muhammad Bin Sireen, da Hasanul Basriy, da Ishaq Bin Raahawaih, ita ce kuma zabin Shaikhul Islam Bin Taimiyyah da kuma Ibnul Qayyim, da Uthaimeen. Wata kila su suna ganin cewa wannan hadithin da muka ambata bai inganta ba.
3. Lalle mazhabar Jumhur da dalilansu su ne suka fi karfi in sha Allahu Ta’aa’laa.