1. Kungiyoyi ne guda biyu’ kuma ko wacce daga cikinsu tana zaman kanta, tare da tsarinta, dayar sunanta: “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah”, dayar kuma sunanta: “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah Wacce Sheikh Isma’ila Idris ya kafa”.

2. Ita Kungiyar “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah” an kafata ne a ranar 12/3/1978, kuma Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta yi mata register, ta ba ta certificate a ranar 11/12/1985, shi kuma wannan certificate din tunda aka ba da shi yana nan a gurin Shugaban kungiyar na kasa baki daya Alhaji Musa Muhammad Maigandu har lokacin da Allah Ya yi masa rasuwa, sannan bayan mutuwarsa ta koma hannun wanda ya gaje shi watau Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau.

3. Ita kuma Kungiyar “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah Wacce Sheikh Isma’ila Idris ya kafa”, Shi Sheikh Isma’ila Idris din ya kafata ne a 1991, bayan da Majalisar Zartaswa ta Kungiyar “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah” wacce take da register da certificate daga Gwamnatin Tarayyar Nigeria da sauke shi daga mukamin shugaban Majalisar Masu wa’azi (malamai) na Kungiyar a ranar 26/8/1991, ta kuma nada Sheikh Muhammad Rabi’u Daura a kan mukamin.

4. Ni dai a iya sanina har yau din nan wannan Kungiya ta “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah Wacce Sheikh Isma’ila Idris ya kafa” ba ta da register da certificate daga Gwamnatin Tarayyar Nigeria.

5. Mu membobin “Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah” muna gina mu’amalarmu ne da sauran kungiyoyin da ake da su cikin gida Nigeria da ma wajenta a bisa abin da ya dace da Alkur’ani da Hadithi da kuma tsarin gudanar da Nigeria.

6. Allah muke roko da Ya taimake mu har kullum.

4 Comments

  1. This is the right blog for anyone who wants to find out about this topic. You realize so much its almost hard to argue with you (not that I actually would want…HaHa). You definitely put a new spin on a topic thats been written about for years. Great stuff, just great!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *