1. Har kullum ‘yan bidi’a da sauran jinsin batattu su kan yi amfani ne da kalmomi mara fasaha da balaga domin karfafa bidi’arsu da batarsu; saboda su kalmomi masu cike da balaga da fasaha da Shari’a ke amfani da su ba za su taimaka musu ba cikin yada wata bata tasu, ko yada wata bidi’a tasu.
2. Misali, a cikin Alkur’ani da ingantattun hadithan Annabi mai tsira da aminci babu inda aka yi umurni da tsiraitacciyar haduwa, ko da tsiraitaccen hadin kai ba, dalilin da ya sa hakan kuwa shi ne: babu talazumi tsakanin samuwar tsiraitaccen hadin kai, ko tsiraitacciyar haduwa da kasancewar mutum a bisa tafarkin Shari’a, idan kana son ka fahimci wannan bayani sosai sai ka dubi group din ‘yan fashi da makamai za ka ga cewa suna iya hada kai a tsakaninsu su rika yin fashi suna kashe mutane suna kwace musu dukiyoyinsu, amma kuma wannan haduwa tasu, ko wannan hadin kai nasu ba zai iya fidda su daga cikin sabon Allah ba, a’a ga shi dai sun hada kan amma kuma suna cikin sabon Allah dumu dumu.
Haka nan za a iya samun wasu group na ‘yan bidi’a su hada kai cikin yada bidi’arsu da yin riko da ita sau da kafa, amma kuma irin wannan haduwa, ko irin wannan hadin kai ba ya iya fidda su daga cikin sabon Allah, a’a sai ma dai ya kara dulmuyar da su a cikinsa.
Ke nan babu masu nacewa a kan yin kira zuwa ga tsiraitacciyar kalmar haduwa, ko tsiraitacciyar kalmar hadin kai sai i
rikitattun da suka jahilci manufar Shari’ar Musulunci.
3. Allah Ya kira mutane ne zuwa ga yin riko da igiyar Allah; watau Alkur’ani da Hadithi, a inda ya ce: ((واعتصموا بحبل الله جميعا ولا تفرقوا)) ((Ku yi riko da igiyar Allah gaba daya kada ku rarraba “ga barinta”)). Ya kuma ce: ((وان هذا صِرَاطِي مستقيما فاتبعوه ولا تتبعوا السبل فتفرق بكم عن سبيله)) ((Kuma wannan hanyata ce wacce take mikakkiya sai ku bi ta, kada ku bi hanyoyin sai su raba ku da hanyata)).
Ma’anar Kalmar “Hablullahi” ita ce ma’ar kalmar “Siraatii Mustaqiiman”.
Wadannan kalmomi su ne Shari’a take yin amfani da su saboda irin yawan fasaha da balaga da ke cikinsu; saboda kasancewarsu har kullum tsantsar shiriya da tsantsar alheri.
Tabbas ranar da duk group din ‘yan fashi da makamai suka yi riko da igiyar Allah gaba daya to kuwa a ranar sun bar yin fashi da makami ke nan.
Tabbas a ranar da duk wasu karkatattu, ko wasu ‘yan bidi’a suka yi riko da igiyar Allah, to kuwa shi ke nan a ranar sun bar bidi’ar da karkatar ke nan.
Allah muke roko da Ya ba mu ikon yin riko da igiyar Allah cikin Aqida, da Ibada, da Mu’amala, Ya kuma tsare mu daga fadawa cikin sharrin bidi’a da jahilci. Ameen.
You made some nice points there. I did a search on the subject matter and found most individuals will consent with your site.
This actually answered my problem, thanks!