Abin da shugaban America Donald Trump ya yi na karɓar sharri, da ƙage, da ƙaryar da shugabannin ƙungiyar CAN suka sharara wa Duniya na cewa wai musulmin Nigeria suna yi wa kiristocin Nigeria kisan ƙare dangi shi ne asalin aƙidar kirista a duk inda yake a Duniyan nan sai ƴan kaɗan da Allah Ya kuɓutar daga cikinsu!!
Mu da ma can Ubangijinmu Ya gaya wa Annabinmu da ma kowa daga cikinmu a cikin Alƙur’aninSa mai girma, a Suratul Baƙarah Ayah ta 120 cewa: ((Har abada Yahudawa da Kiristoci ba za su yarda da kai ba har sai ka bi addininsu tukun, to ka ce: Lalle shiriyar Allah ita ce Shiriya)). ((ولن ترضى عنك اليهود ولا النصارى حتى تتبع ملتهم قل إن هدى الله هو الهدى)).
Yanzu dai ni a ganina sai dukkanmu ƴan Nigeria musulminmu da kiristocinmu mu shirya wa fiskantar musibar rayuwa da za ta same mu saboda zaluncin Donald Trump da zai tinƙare mu, zaluncin da shi Trump ɗin zai gina shi a kan ƙarairayin da ƙungiyar CAN ta Nigeria ta sharara wa Duniya.
Allah muke roƙon Ya taimaki ƴan Nigeria Ya kuɓutar da su daga sharrin dukkan wani mai sharri a Duniyan nan. Ameen.