1. Ya Allah Ka karfafa mana Musuluncinmu, da imaninmu, da tsayuwarmu a kan sunnar annabinmu Mai tsira da aminci.
2. Ya Allah shugaban kasarmu da mataimakinsa da sauran jami’ansa Ka taimake su Ka yi musu jagoranci ta yadda shugabancinsu zai yi albarka ya zamanto alheri mai yawa ga kasarmu Nigeria da kuma dukkan ‘yan kasarmu.
3. Ya Allah Ka taimake mu Ka bunkasa tattalin arzikin kasarmu tare da tattalin arzikin daidaikunmu, Ka taimake mu Ka daukaka darajar kudin kasarmu Naira.
4. Ya Allah Ka sanya albarka cikin kasuwancin ‘yan kasuwanmu, da noman manomanmu, da kiwon makiyayanmu, da sana’ar masu san’armu, da aikin ma’aikatanmu, da karatun ‘yan makarantanmu, da dukkan lamuranmu. Ameen.