Jiya na saurari maganar shugaban masu karyata hadithan Manzon Allah na garin Kaduna, a inda yake bayanin hujjar haramcin cin naman kare da naman jaki a cikin Alkur’ani mai girma, a inda ya ce Allah Ya kamanta wanda ya kafurce wa ayoyinSa da kare, a inda Ya ce a cikin Alkur’ani:-
((واتل عليهم نبأ الذي ءاتيناه ءاياتنا فانسلخ منها فأتبعه الشيطان فكان من الغاوين. ولو شئنا لرفعناه بها ولكنه أخلد إلى الأرض واتبع هواه فمثله كمثل الكلب إن تحمل عليه يلهث أو تتركه يلهث ذلك مثل القوم الذين كذبوا بئايات الله فاقصص القصص لعلهم يتفكرون)).
Sai wannan jahili murakkabi ya ce: a cikin wadannan ayoyi biyu na suratul A’araf aya ta 175-176 Allah Ya nuna munin kare Ya kamanta wanda ya kafurce wa ayoyin Allah da shi karen ta hanyar siffarsa ta lallage a ko da yaushe. Ya ce tunda Allah ya siffanta mai kafirce wa ayoyin Allah da kare; ke nan cin naman kare haramun ne!!
Amma kuma abin mamaki shi wannan jahili murakkabi na garin Kaduna wanda yake ikirarin cewa shi ba ya yin imani da Hadithi sai Alkur’ani kawai, ya manta da cewa Allah Ya siffanta kafuran Aljannu da kafuran Mutane da dabbobin ni’imah watau Rakuma da Shanu da Tumaki da Awaki a aya ta 179 cikin ita dai wannan Surah ta A’araf a inda Ya ce:-
((ولقد ذرأنا لجهنم كثيرا من الجن والإنس لهم قلوب لا يفقهون بها ولهم أعين لا يبصرون بها ولهم ءاذان لا يسمعون بها اولئك كالأنعام بل هم أضل اولئك هم الغافلون)).
Duk da kuma wannan kamanci da Allah Ya bayyana cikin wannan Ayar shi wannan dan kalakaton yana ganin halaccin cin naman rakuma da shanu da tumaki da awaki!!
Toh amma idan wannan jahili murakkabi ya ce: ai Allah Ya halatta cin dabbobin ni’ima cikin wasu ayoyi daban. Toh sai a ce da shi: Ke nan hakan ya tabbatar da cewa mujarradin kamanta wata dabba da wani kafiri ko wasu kafurai ba ya nuna haramcin ita dabbar, wannan kuwa yana tabbatar da cewa ke nan babu nassin Alkur’ani mai girma a kan haramta cin naman kare ko cin naman jaki.
Haka nan wannan jahili murakkabin ya haramta cin naman jaki saboda aya ta 5 a cikin suratul Jumu’ah watau:-
((مثل الذين حملوا التوراة ثم لم يحملوها كمثل الحمار يحمل أسفارا بئس مثل القوم الذين كذبوا بئايات الله والله لا يهدي القوم الظالمين)).
Amsarmu a kan wannan mas’ala ta cin naman jaki ita ce amsarmu da muka gabatar a sama a kan cin naman kare.
Allah muke rokon Ya tsare al’ummarmu daga fada wa cikin wannan bidi’a ta ikirarin yin imani da Alkur’ani kawai banda ingantattun hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Ameen.