1. Yana da kyau ‘yan’uwa su san cewa duk da yawan sharrin da masu biye wa majusawan kasar Iran ke yadawa game Sahabban Manzon Allah mai tsira da aminci, Shi Sayyidina Aliyyu da kuma Sayyidina Mu’awiyah bayan kasancewar ko wane daya daga cikinsu musulmi ne, toh kuma su biyun har yanzu ‘yan’uwan juna ne na jini, sun hadu a kan kakansu Abdu Manaf.
2. Shi dai Abdu Manaf shi ne kaka na uku ga Sayyidina Aliyyu, kuma kaka na hudu ga shi Sayyidina Mu’awiyah. Ga ma yadda nasabar tasu take:-
(1) Aliyyu Dan Abu Talib, Dan Abdul Muttalib, Dan Hashim, Dan Abdu Manaf.
(2) Mu’awiyah Dan Abu Sufyan, Dan Harb, Dan Umayyah, Dan Abdu Shams, Dan Abdu Manaf.
3. Dukkansu biyun watau Sayyidina Aliyyu da Sayyidina Mu’awiyah suna daga cikin zababbiyar nasabar nan ta Annabi Ibrahim alaihis salam, da zababbiyar nasabar nan ta Annabi Isma’ila alaihis salam, da zababbiyar nasabar nan ta Kinanah, da zababbiyar nasabar nan ta Quraish watau Fihr. Kamar yadda Imamu Muslim da Tirmiziy da Ahmad da Ibnu Hibban suka ruwaito daga Waa’ilah Bin Asqaa cewa Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce:
((ان الله اصطفى من ولد إبراهيم اسماعيل واصطفى من ولد إسماعيل بني كنانة واصطفى من بني كنانة قريشا واصطفى من قريش بني هاشم واصطفاني من بني هاشم)).
((Lalle Allah Ya zabi Isma’il daga cikin ‘ya’yan Ibrahim, Ya kuma zabi Banu Kinanah daga cikin ‘ya’yan Isma’il, Ya kuma zabi Quraish (watau Banu Fihr) daga cikin Banu Kinanah, Ya kuma zabi Banu Hashim daga cikin Quraish, Ya kuma zabe ni daga cikin Banu Hashim)).
4. Lalle an yi yaki a tsakanin Sayyidina Aliyyu da magoya bayansa da kuma Sayyidina Mu’awiyah da magoya bayansa na ‘yan shekaru a kan harkar jagoranci, toh amma wannan yakin da ya gudana a tsakanin rundunonin guda biyu bai fitar da ko wanne daga cikinsu ba daga da’irar Musulunci da Imani; kamar yadda za a iya fahimta daga fadar Allah cikin suratul Hujurat aya ta 9:-
((وإن طائفتان من المؤمنين اقتتلوا فأصلحوا بينهما فإن بغت إحداهما على الأخرى فقاتلوا التي تبغي حتى تفيء إلى امر الله فإن فاءت فأصلحوا بينهما بالعدل وأقسطوا إن الله يحب المقسطين)).
((Idan bangarori biyu daga cikin Muminai suka shiga yakar juna toh ku sulhunta tsakaninsu, idan daya ta yi zalunci a kan dayar toh ku yaki wacce ta yi zaluncin har sai in ta dawo zuwa ga umurnin Allah, toh idan ta dawo sai ku sulhunta tsakaninsu da adalci, ku yi adalci, lalle Allah Yana son Adilai)). Kun gani a nan yakin da ya gudana a tsakanin bangarori biyun bai fitar da su daga Imani ba; domin Allah Ya siffanta dukkan bangarori biyun da Imani, Ya kuma kira su da suna Muminai; saboda haka mujarradin yaki da juna kawai saboda jagorancin duniya ko wani abu mai kama da shi ba ya kore Imani da Musulunci daga bangarorin da suka yaki junansu.
5. Idan kuma wani ya ce: Toh ai Annabi ya ce cikin Sahihu Muslim hadithi na 78 “Babu mai son Aliyyu sai mumini, babu kuma mai kin shi sai munafuki”. Ke nan wadanda suka yake shi sun ki shi ne, tunda kuma suka ki shi toh shi ke nan sun zama munafukai kafurai!! Idan wani ya fadi irin wannan magana ta rashin fahimtar Addini sai a ba shi amsa da cewa: Kada ya manta da cewa Buhariy ya ruwaito hadithi na 3,783, da Muslim na 75 daga Baraa Bin Azib cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: “Babu mai son Ansar sai mumini, babu mai kin Ansar sai munafuki”. Haka nan Muslim ya ruwaito hadithi na 2,491, da Ahmad na 8,259, da Ibnu Hibban na 7,154, da Bazzar na 9,387, da Tabaraniy na 76 cewa bayan Annabi mai tsira da mincin Allah ya yi wa Abu Hurairah addu’a shi ke nan babu wani muminin da za a halitta wanda zai ji labarin shi Abu Hurairah ko kuma ya gan shi da idon shi fashe sai ya so shi”. In dai ka ga mutum yana kin Abu Hurairah ke nan ba mumini ba ne shi.
5. Saboda haka abin da irin wadannan Hadithai suke nufi ba shi ne abin da Jahilai da wasu ‘yan bidi’ah suke nufi ba. Hafiz Ibnu Hajar ya ce cikin Fathul Bariy1/63: Wadannan Hadithai suna nufi ne idan mutum ya ki wadannan mutanen ne saboda kawai suna son Allah da ManzonSa ko saboda suna taimakon Allah da ManzonSa, ko kuma kawai saboda suna ‘yan’uwa ne na jini ga shi Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, toh amma in har ya zamanto saboda wani dalili ne kawai da yake iya sa dan Adam da wani dan’uwansa dan Adam su yi rikici toh wadannan Hadithai ba sa nuni a kan wannan ma’ana.
6. A karshe muna kara nanatawa cewa lalle abu ne mai kyau al’ummar Musulmi a duk inda suke su kasance masu fadaka; domin kada su fada cikin tarkon da mabiya majusawan Iran suke dana musu domin su raba su da asalin Musuluncin da Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ya zo musu da shi.