
1. Shari’ar Musulunci tana ƙiran Sunnar Annabi صلى الله عليه وآله وسلم da suna Littafin Allah, kamar yadda take ƙiran Alƙur’ani mai girma da suna Littafin Allah; saboda haka duk wanda ya ƙaryata Sunnah to kuwa tabbas ya ƙaryata Littafin Allah, wanda kuwa ya ƙaryata Littafin Allah to tabbas ya kafirta.
2. Idan kana son ka gane cewa Sunnar Manzon Allah Littafin Allah ne a cikin sauƙi sai ka karanta ayah ta 36 cikin Taubah:
((إن عدة الشهور عند الله اثنا عشر شهرا في كتاب الله يوم خلق السماوات والأرض منها أربعة حرم فلا تظلموا فيهن أنفسكم)).
Sannan sai kuma ka karanta hadithi na 3,197 cikin Buhari, na 1,679 cikin Muslim inda Annabi ya ce:
((الزمان قد استدار كهيءته يوم خلق السماوات والأرض السنة اثنا عشر شهرا منها أربعة حرم ثلاثة متواليات ذو القعدة وذو الحجة والمحرم ورجب الذي بين جمادى وشعبان)).
3. Kamar yadda kuka gani a nan Allah Ya ce a cikin Alƙur’ani: A cikin Littafin Allah akwai wata 12 cikin shekara, sannan daga cikin 12 ɗin akwai 4 da aka haramta yin yaƙi a cikinsu, to amma kuma sunan watan Ramadan ne kaɗai Alƙur’ani ya ambata, bai ambaci sauran 11 ɗin ba, bai kuma ambaci 4 ɗin ba, to amma Sunnah ita ce ta ambaci Watanni 11 da suka sauran, kuma ita ce ta ambaci sunayen watanni 4 ɗin da aka haramta yaƙi a cikinsu; ke nan Sunnar Manzon Allah Littafin Allah ne da nassin Alƙur’ani.
4. Wannan hujja wacce take ƙarara tamkar Rana tana wajabta wa dukkan mai son shiga Aljanna ya yi sauri ya yi imani tare da yin aiki da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah, kada ya biye wa mulhidai masu ƙiran mutane zuwa ga kafirce wa Sunnah
.