Shi’ah Rafidha sun ce wa Duniya limamansu 12 sun fi Annabawa daraja in banda Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم haka nan suna cewa yin imani da su da yarda da ismarsu da yin musu biyayya wajibi ne kuma sharadin shiga Aljannah ne!

Sai dai kuma abin mamaki shi ne: Babu sunayen wadannan limamai nasu 12n cikin Alkur’ani mai girman da yake shi ne babban masdarin Musulunci, haka nan babu maganar cewa su wadannan 12n ma’asumai ne, haka nan babu maganar wajibcin yin musu biyayya a cikinsa;  duk kuwa da cewa dukkan usul na imani da Musulunci ya zo da su, watau yin imani da Allah da mala’ikunsa da littattafanSa da manzanninSa, da ranar Lahira da qaddara, ko wanne ne daga cikin wadannan Usul na Imani an yi bayaninsa fillafilla a cikin shi Alkur’ani, toh amma sai ga wani Asli babba da Shi’ah Rafidha suka kirkiro babu shi babu labarinsa a cikin wannan Littafi mai yawan girma!!

Misali: Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Surar Baqarah ayah ta 136:
((قولوا آمنا بالله وما أنزل إلينا وما أنزل إلى إبراهيم وإسماعيل وإسحاق ويعقوب والأسباط وما أوتي موسى وعيسى وما أوتي النبيون من ربهم)).
Ya kuma ce har yanzu:
)) ليس البر ان تولوا وجوهكم قبل المشرق والمغرب ولكن البر من ءامن بالله واليوم الاخر والملايكة والكتاب والنبيين)) (( ءامن الرسول بما انزل اليه من ربه والمؤمنون كل ءامن بالله وملايكته وكتبه ورسله))
da sauran ayoyi da yawan gaske a cikin wannan babi na bayanin Usul din Imani, amma abin mamaki sam
babu ambaton limaman shi’ah 12 da suka kirkira wa kansu a cikinsa!!

2 Comments

  1. I’ll right away grab your rss as I can not in finding your email subscription hyperlink or newsletter service. Do you have any? Kindly permit me realize in order that I may subscribe. Thanks.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *