BA SU DA MAFAKA SAI SUN DAWO KAN SUNNA:

1. Masu raba kafa su bi Sunnah cikin wasu mas’alolin Shari’ah, sannan su juya wa Sunnah baya cikin wasu mas’alolin Shari’ah, tabbas ba su da wata mafaka har sai sun dawo sun bi Sunnah dodar cikin dukkan mas’alolin.

2. Shekaran jiya Lahadi na dan tattauna a Facebook da wani bawan Allah mai ganin cewa yin Sadlu cikin salla Sunnah ce, duk kuwa da cewa abin da Sunnah Kauliyyah da Sunnah Fi’iliyyah suka zo da shi cikin Hadithai inagantattu shi ne yin Kablu kadai ba wai yin Sadlu ba. Hujjar wannan bawan Allah ita ce an samu wasu a’athar da suke cewa wasu daga cikin Sahabbai da Tabi’ai da Tabi’ut Tabi’in Sadlu suke yi a cikin sallarsu, tunda kuwa Sadlu suke yi a cikin sallarsu wannan ya nuna ke nan yin Sadlu cikin salla shi ma Sunnah ce!

3. Ke nan wannan bawan Allah da muka tattauna da shi, tare da sauran ire irensa su sun daidaita karfin aikin Annabi mai tsira da aminci da kuma karfin umurninsa ga al’ummar Duniya sun daidaita su iyazan billah da karfin ayyukan wasu Salafus Salih; saboda sun ce kamar yadda Kablu yake Sunnah haka shi ma Sadlu yake Sunnah, ko wane daya ka yi daga cikinsu toh ka yi Sunnah ne sam ba ka saba wa Sunnar Manzon Allah mai tsira da aminci ba!!

4. Amma kuma, abin mamaki shi wannan bawan Allah ya yarda da cewa taron Suna bidi’ah ce da ta saba wa Sunnah Tarkiyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah, duk kuwa da cewa an samu wani athar da ya nuna cewa wasu Tabi’ai tare da wasu Sahabbai sun yi taron sunan, wannan atharin kuwa shi ne athari na 348 da Imamul Bukhariy ya ruwaito cikin littafinsa Al-Adabul Mufrad daga Mu’awiyah Bin Qurrah:-
‎عن معاوية بن قرة يقول لما ولد لي اياس دعوت نفرا من اصحاب النبي صلى الله عليه وسلم فاطعمتهم فدعوا فقلت انكم قد دعوتم فبارك الله لكم فيما دعوتم واني ادعو بدعاء فأمنوا. قال فدعوت له بدعاء كثير في دينه وعقله)).
Ma’ana: ((Daga Mu’awiyah Bin Qurrah yana cewa lokacin da aka haifa mini Iyas na gayyato wasu mutane daga cikin sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah na ciyar da abinci, suka kuma yi addu’a, sai na ce lalle ku kun yi addu’a Allah ya yi muku albarka cikin addu’ar da kuka yi, kuma lalle ni ma zan yi wata addu’a kuma ku rika cewa a’amin. Sai ya ce sai na yi masa (jaririn) addu’a mai yawa game da addininsa da kuma hankalinsa)).

5. Wannan bawan Allah shi da ire irensa sun yarda su jingine Sunnah Kauliyyah da Sunnah Fi’iliyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah gefe guda, su koma su yi riko da abin da suka ce aiki ne na wasu Sahabbai da wasu Tabi’ai wanda kuma ya yi hannun riga da wannan Sunnah ta Manzon Allah, sun yarda su yi haka cikin abin da ya shafi Kablu da Sadlu!! Amma kuma suka kasa jingine Sunnah Tarkiyyah ta Annabi mai tsira da amincin Allah a gefe guda, su koma su yi aiki da wani athari daga wasu Tabi’ai da Sahabbai cikin abin da ya shafi taron Suna!! Watau a wannan babi na taron suna sun yarda da cewa shi taron suna bidi’a ce saboda ya saba wa Sunnah Tarkiyyah ta Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, koda yake an samu wadanda suka yi shi cikin Salafus Salih.

6. Gaskiyan Al’amari shi ne wannan bawan Allah tare da ire irensa ba su da wata mafaka a mahangar Shari’ar Musulunci har sai sun hada kafafuwansu guri guda tukun sun bi ka’idar Ilmi dodar, sun gabatar da Sunnar Annabi, sawaa’un Kwuliyyah ce ita, ko Fi’iliyyah ce ita, ko kuwa Tarkiyyah ce ita, a kan dukkan wani abu da ya saba mata na maganar wani mutum, sawaa’un cikin Salafus Salihi ne ko kuwa cikin wanin Salafus Salihi ne. Musamman ma da yake su Salafus Salihi sun riga sun gaya wa Duniya cewa a duk lokacin da suka yi wata magana, ko wani aiki sannan aka ga ya saba wa na Manzon Allah toh maza maza a yi watsi da nasu a dawo a yi riko da na Manzon Allah; domin Manzon Allah shi ne kadai Allah Madaukakin Sarki Ya aiko zuwan ga al’ummar Duniya ba wai waninsa ba. Allah muke rokon Ya taimake mu. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *