1. A dai cikin littattafanmu na Ahlus Sunnah wal Jama’a babu hadithi ingantacce ko da daya ne da ya zo da halaccin ko da umurnin yin sadlu a cikin salla. Amma an samu hadith maudhuu’i watau hadithin karya guda daya da zahirinsa yake nuna halaccin yin sadlu a cikin salla.
2. Imamut Tabaraniy ya ruwaito cikin Mu’ujamul Kabir hadithi na 139, daga Khaseeb Bin Jahdar daga Nu’uman Bin Nu’aim daga Abdurrahman Bin Ganm daga Mu’az Bin Jabal cewa: ((كان النبي صلى الله عليه وسلم اذا كان في صلاته رفع يديه قبالة اذنيه فاذا كبر أرسلهما ثم سكت وربما رأيته يضع يمينه على يساره)). Ma’ana: ((Annabi mai tsira da aminci ya kasance idan ya kasance cikin sallarsa sai ya daga hannayensa biyu zuwa gaban kunnuwansa, idan ya yi kabbara sai ya sake su, sai kuma ya yi sit, tana yiwuwa ma in gan shi yana dora damansa a kan hagunsa)).
3. Haithamiy ya ce cikin Majma’uz Zawaa’id 2/102: ((A cikin isnadinsa akwai Khaseeb Bin Jahdar, makaryaci ne shi)). Ibnul Mulaqqan ya ce cikin Al-Badrul Muneer 3/515: ((Cikin isnadinsa akwai Khaseeb Bin Jahdar, tabbas Shu’ubah da Qattan sun karyata shi)). Hafiz Ibn Hajar ya ce cikin At-Talkheesul Habeer 1/550: ((A cikin isnadinsa akwai Khaseeb Bin Jahdar, tabbas Shu’ubah da Qattan sun karyata shi)).
4. Lalle mu ba mu da nufin kome sai kokarin sanya mutane a kan hanya; domin a gudu tare a kuma tsira tare. Allah Ya taimake mu. Ameen.
Masha Allah
I don’t think the title of your article matches the content lol. Just kidding, mainly because I had some doubts after reading the article.