1. Duk yawan ibadar mutum, duk yawan lkhlasinsa (tsarkake niyyarsa) a cikin ibadar, matukar bai yi ta a bisa sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ba, to babu ruwan Annabi mai tsira da amincin Allah da shi.

2. Bukhariy ya ruwaito hadithi na 5063, da Muslim na 1401 daga Anas Bin Malik Allah Ya kara masa yarda cewa: wasu mutum uku, sun zo gidajen matan Annabi mai tsira da amincin Allah, suna tambaya game da ibadar Annabi mai tsira da amincin Allah, lokacin da aka ba su labari, sai suka ga kamar ibadar ta yi kadan; sai suka ce: Ai ba za mu hada kanmu da Annabi mai tsira da amincin Allah ba; domin shi an riga an gafarta masa zunubansa da suka gabata da ma masu zuwa nan gaba. Sai dayansu ya ce: Lalle ni tabbas zan rika yin sallar dare (na dukkan dare). Dayan kuwa sai ya ce: Zan rika azumtar ko wace rana ba zan taba fashi ba. Dayan kuwa ya ce: Zan nisanci mata har abada ba zan yi aure ba. Sai Annabi mai tsira da da amincin Allah ya zo gurinsu ya ce: Ku ne wadanda kuka ce: kaza da kaza? To ina rantsuwa da Allah, lalle ni na fi ku tsoron Allah da takawa, amma kuma ina yin azumi ina kuma ajiyewa, ina kuma sallar dare ina kuma yin barci, ina kuma auren mata. Duk wanda ya kyamaci sunnata ba ruwana da shi)).
((جَاءَ ثَلَاثَةُ رَهْطٍ إلى بُيُوتِ أزْوَاجِ النَّبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم، يَسْأَلُونَ عن عِبَادَةِ النَّبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم، فَلَمَّا أُخْبِرُوا كَأنَّهُمْ تَقَالُّوهَا، فَقالوا: وأَيْنَ نَحْنُ مِنَ النَّبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم؟! قدْ غُفِرَ له ما تَقَدَّمَ مِن ذَنْبِهِ وما تَأَخَّرَ، قالَ أحَدُهُمْ: أمَّا أنَا فإنِّي أُصَلِّي اللَّيْلَ أبَدًا، وقالَ آخَرُ: أنَا أصُومُ الدَّهْرَ ولَا أُفْطِرُ، وقالَ آخَرُ: أنَا أعْتَزِلُ النِّسَاءَ فلا أتَزَوَّجُ أبَدًا، فَجَاءَ رَسولُ اللَّهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم إليهِم، فَقالَ: أنْتُمُ الَّذِينَ قُلتُمْ كَذَا وكَذَا؟! أَمَا واللَّهِ إنِّي لَأَخْشَاكُمْ لِلَّهِ وأَتْقَاكُمْ له، لَكِنِّي أصُومُ وأُفْطِرُ، وأُصَلِّي وأَرْقُدُ، وأَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، فمَن رَغِبَ عن سُنَّتي فليسَ مِنِّي)).

3. Sai ku lura da kyau, wadannan Sahabbai uku ko wannensu ya kudurci yin aikin ibada mai yawan gaske tare da yin lkhlasi cikin ibadar, to amma tunda babu Sunnah cikin ibadar, akwai kyamatar Sunnah tare da masu ibadar, sai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce babu ruwan shi da su. Lalle wannan al’amari zai wajabta mana yin riko da Sunnah cikin aqidarmu, da ibadarmu, da kuma mu’amalarmu, tare da nuna gamsuwa a kan cewa lalle lazimtar Sunnah ita ce kadai mafita a garemu.

4. Allah muke rokon Ya cusa son bin sunnar ManzonSa cikin zukatan al’ummarmu, Ya kuma cusa kin bidi’ah cikin zukatan nasu. Ameen.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *