Cikin kokarin da Shi’ah Rafidhawa suke yi na rusa jauharin Musulunci ta hanyar zubar wa Sahabbai mutunci da kafrta su; Sahabban nan dai da suka yada Musulunci zuwa sassan  Duniya su ne da suke kafrtawa da sunan nuna soyayya ga Manzon Allah da iyalansa!! Wani mulhidi daga cikin wadannan Rafidawan bayan da ya gama la’antar Sayyidina Abubakar da kafirta shi sai kuma ya koma yana ta yabon Sayyidina Ali yana cewa saboda yawan darajarsa da girmansa da sadukarwarsa a lokacin da Manzon Allah ya zo yin hijira shi ne ya bari a kan shimfidarsa!

Wannan jahilin barafidhe miskini bai san cewa ba a dai wannan batu na hijirar Manzon Allah daga Makka zuwa Madina duk daraja daya da Sayyidina Ali zai samu saboda ita, toh kuwa a hankalce ya kamata a ce Sayyidina Abubakar ya samu ninkinta; saboda dalili kamar haka:

Dalili na farko shi ne: Su kafuran Makka sam da ma ba Ali ba ne suke nema su kashe ko su daure, a’a Manzon Allah ne suke nema su kashe ko su daure; wannan shi ne ma ya sa da ba su sami Annabin ba sam ba su ma kula da shi Aliyu Bin Abi Talib ba ballanta ma su daure shi ko kuwa su kashe shi, fita sha’aninsa kawai suka yi suka koma suna neman inda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yake domin du cutar da shi.

Dalili na biyu shi ne: Su kafiran Makkah Annabi ne suke nema domin su kashe ko su daure, ke nan tabbas duk wanda suka same shi tare da shi Annabin a hanyar zuwa Madina a hankalce dai duk abin da ya sami shi Annabi na musiba toh shi ma zai same shi; ke nan wanda ke tare da Annabi a irin wannan shi ne ya kamata a siffanta shi da siffar sadaukar da kai domin kare Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba wani wanda ke kwance a gida a kan shmfida ba.

Dalili na uku shi ne: Shi Sayyidina Abubakar shi ne yake cikin hatsari da wahala; domin shi ne ya bar gidansa da iyalansa domin ya kare Manzon Allah da Musulunci, amma shi Sayyidina Ali ba yi ma da Iyalin sam domin shi a wannan lokaci mutum ne da yake dan saurayin da bai wuce dan shekara 23 ba, kuma babu inda ya je, sam bai sha wahalar hawa dutse da shiga kogo ba, haka nan bai zuuna cikin kogo na kwanaki cikin kunci ba, haka nan bai yi tafiya daga Makkah zuwa Madinah na makonni da yawa ba.

Dalili na hudu shi ne: Babu inda Alkur’ani mai girma ya ya yi maganar shi Sayyidina Ali game da wannan hadathan, amma ya yi maga game da Sayyidina Abubakar game da wannan Hadithan da kuma irin lafazin da cikin dukkan Alkur’ani ba a yi amfani da shi ba sai a lokacin da ake son Akwatar wa mumuni hankalinsa, a lokacin da ake son a nuna cewa ana tare da shi, wannan lafazin kuwa shi ne: لا تحزن kada ka yi bakin ciki kanar dai yadda ya zo cikin suratut Taubah aya ta 40 inda Allah ya ce:
((إلا تنصروه فقد نصره الله إذ أخرجه الذين كفروا ثاني اثنين إذ هما في الغار إذ قال لصاحبه لا تحزن إن الله معنا)). التوبة: ٤٠.
Tarjama: ((Idan har ba ku taimake shi ba toh lalle Allah Ya taimake shi a lokacin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun mutum biyu a lokacin da su biyun suke cikin kogo a lokacin da ya gaya wa sahibinsa kada ka yi bakin ciki lalle Allah Yana tare da mu)). Ku lura da kyau za ku ga cewa duk cikin Alkur’ani mai girma in ka ga an yi amfani da wannan lafazi na لا تحزن toh ana so ne akwantar wa mumini mutumin kirki hankali. Ga wasu ayoyi kamar 13 zan kawo su a matsayin misali kawai:-
((ولا تمدن عينيك إلى ما متعنا به أزواجا منهم ولا تحزن عليهم واخفض جناحك للمؤمنين)). الحجر: ٨٨.
((واصبر وما صبرك إلا بالله ولا تحزن عليهم ولا تك في ضيق مما يمكرون)). النحل: ١٢٧.
((فرجعناك إلى أمك كي تقر عينها ولا تحزن…)). طه: ٤٠.
((ولا تحزن عليهم ولا تكن في ضيق مما يمكرون)). النمل: ٧٠.
((فرددناه إلى أمه كي تقر عينها ولا تحزن..)). القصص: ١٣.
((وقالوا  لا تخف ولا تحزن إنا منجوك وأهلك إلا امرأتك كانت من الغابرين)). العنكبوت: ٣٣.
((ولا تهنوا ولا تحزنوا وأنتم الاعلون إن كنتم مؤمنين)). ءال عمران: ١٣٩.
((فاثابكم غما بغم لكي لا تحزنوا على ما فاتكم ولا على ما أصابكم)) ءال عمران: ١٥٣.
((إن الذين قالوا ربنا الله ثم استقاموا تتنزل عليهم الملائكة الا تخافوا ولا تحزنوا )) فصلت: ٣٠.
((ادخلوا الجنة لا خوف عليكم ولا أنتم تحزنون)). الأعراف: ٤٩.
((يا عباد لا خوف عليكم  اليوم ولا أنتم تحزنون)) الزخرف:٦٨•
((فناداها من تحتها ألا تحزني قد جعل ربك تحتك سريا)) مريم ٢٤.
((فإذا خفت عليه فالقيه في اليم ولا تخافي ولا تحزني)). القصص ٧.

Lalle idan kuka nitsu za ku fahimci cewa: A duk lokacin da Rafidhawa suka ambaci wani abin yabo domin su yabi Sayyidina Aliyyu da shi, toh lalle ne za ku tarar da cewa Sayyidina Abubakar ya mallaki ninkin irin wannan abin yabon. Haka nan a duk lokacin da suka ambaci wani abin zargi domin su zargi Sayyidina Abubakar da shi toh tabbas za ku tarar da cewa akwai ninkin irin wannan abin zargi tare da Sayyidina Ali, in sha Allah wannan tamkar ka’ida ce muttaridah ku rike ta da kyau.

111 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *