Da dai Shi’ah Rafidha mahankalta ne toh da sun fahimci cewa abin da ke lazimtar su shi ne dayan abu biyu: Na farko: Ko dai su fito fili su kafirce wa Alkur’anin da ke hannayensu yanzu; saboda shi Alkur’ani ne da Banu Umayyah mutanen da suke kafurai, maha’inta, la’anannu suka tattara shi, suka rubuta shi, suka ruwaito wa Duniya shi! Abu na biyu shi ne: Su tuba zuwa ga Allah su barranta daga wannan bakar bidi’ah tasu, su dawo su karbi ingantattun hadithan da Ahlus Sunnah suka ruwaito wa Duniya; Ahlus Sunnan nan da suke dauka a matsayin kafurai la’anannun karnukan farautar Banu Umayyah.

Amma ba zai yiwu ba a hankalce dai su yarda da musuluncin Banu Umayyah da imaninsu da amanarsu game da Alkur’anin da suka tattara musu, amma kuma su ki yarda da musuluncinsu da imaninsu da amanarsu game da maganganun Annabi da suka tattara musu.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *