1. Ahmad ya ruwaito Hadithi na 17,193, da Ibnu Khuzaimah Hadithi na 1,938, da Ibnu Hibban Hadithi na 7,210, da Bazzar Hadithi na 4,202, da Dabaraaniy cikin Kabeer Hadithi na 15,031 daga Sahabbai: Al-Irbadh Bin Saariyah, da Abdullahi Bin Abbas, da Abdurrahman Bin Abi Ameerah, da Maslamah Bin Mukhallad cewa: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((اللهم علم معاوية الكتاب والحساب وقه العذاب)).
Ma’ana: ((Ya Allah Ka sanar da Mu’awiyah Littafi, da Hisaabi, Ka kuma tsare shi daga Azaba)). Tabbas addu’ar Annabi karbabbiya ce.
2. Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 4,213, da Ahmad Hadithi na 17,926, da Dabraaniy cikin Al-Ausat Hadithi na 656 daga Sahabi Abdurrahman Bin Abi Ameerah cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce wa Mu’awiyah:-
((اللهم اجعله هاديا مهديا واهد به)).
Ma’ana: ((Ya Allah Ka sanya shi mai shiryarwa, kuma Shiryayye, Ka kuma shiryar ta hanyarsa)). Tabbas addu’ar Annabi karbabbiya ce.
(2). A lokacin da jahilan ‘yan bidi’ah suke kafirta Sayyidina Mu’awiyah suke cewa shi kafiri ne dan Wuta, a dai kuma wannan lokacin ne muke ganin irin yadda Sayyidina Aliyyu yake dabbatar wa duniya da Musuluncinsa da Imaninsa, yake kuma cewa imaninsa bai zarce na shi Mu’awiyah ba duk kuwa da cewa sun yaki junnasu; kuma wannan magana, da wannan tabbacin duk suna cikin littattafan malaman Shi’ah. Misali: Ash-Shareefur Radhiyyu Muhammad Bin Abi Ahmad Al-Husainiy cikin littafinsa Nahjul Balaagah shafi na 448 ya ruwaito daga Sayyidina Aliyyu cewa ya ce game da wadanda suka yi yaki da su a Siffeen:-
((وكان بدء امرنا انا التقينا والقوم من أهل الشام، والظاهر ان ربنا واحد، ودعوتنا في الاسلام واحدة، ولا نستزيدهم في الإيمان بالله والتصديق برسوله، ولا يستزيدوننا، والامر واحد الا ما اختلفنا فيه من دم عثمان، ونحن منه برآء)).
Ma’ana: ((Farkon al’amarinmu shi ne mun hadu a fagen daga mu da mutanen, daga mutanen Sham; alhalin abin da yake zahiri shi ne: Ubangijinmu daya ne, da’awarmu cikin Musulunci daya ce, ba mu zarce su cikin imani da Allah ba da kuma gasgata ManzonSa ba, al’amarin duka daya ne in banda abin da muka yi sabani a cikinsa na jinin Uthman mu kuma kubutattu ne daga gare shi)).
(3). A lokacin da jahilan ‘yan bidi’ah suke kafirta Sayyidina Mu’awiyah suke cewa shi kafiri ne dan Wuta; a dai kuma wannan lokacin ne muke ganin cewa Sayyidina Hasan Bin Aliy yake tabbatar wa duniya cewa: Mu’awiyah shi ne alheri a gare shi a kan ‘yan Shi’an da suke nuna rashin amincewarsu da sulhun da ya yi da shi Mu’awiyan. Misali: babban malamin Shi’ah wanda ya mutu a karni na bakwai na Hijirah Ahmad Bin Aliy Bin Abi Dalib At-Tabarasiy ya ruwaito daga Sayyidina Hasan a cikin littafinsa mai suna: Alih Tijaj 2/290, da Muhammad Baaqir Al-Majlisiy a cikin littafinsa Bihaarul Anwar44/20 cewa Sayyidina Hasan Bin Aliy ya ce:-
((ارى والله معاوية خيرا لي من هؤلاء؛ يزعمون انهم لي شيعة وابتغوا قتلي، وانتهبوا ثقلي، وأخذوا مالي، والله لان أخذ من معاوية عهدا احقن به دمي، وأمن به في اهلي، خير من ان يقتلوني فيضيع أهل بيتي وأهلي)).
Ma’ana: ((Wallahi ina ganin Mu’awiyah ne ya fi min alheri a kan wadannan da suke riya cewa magoya baya suke a gare ni; alhalin sun nemi kashe ni, sun kwace kayayyakina, sun karbe dukiyata. Wallahi in dauki alkawari a gurin Mu’awiyah da zan tsare jinina da shi, na kuma amintu da shi a cikin iyalaina shi ne ya fi mini alheri a kan wadannan su kashe ni mutanen gidana da sauran iyalaina su lalace)).
(4). A lokacin da jahilan ‘yan bidi’ah suke kafirta Sayyidina Mu’awiyah suke cewa shi kafiri ne dan Wuta; saboda rundunarsa ta yi yaki da rundunar Sayyidina Aliyyu a lokacin ne kuma Alkur’ani mai girma, da kuma littattafan Ahlus Sunnah, da ma littattafan Shi’ah
Allah suke tabbatar wa duniya cewa wannan yaki da ya gudana tsakanin wadannan manyan bangarori biyu na Musulmi bai fidda ko wanne daga cikinsu daga Musulunci ko Imani ba a’a ko wanne daga cikinsu yana nan Musulmi yana nan kuma Mumini. Misali ga abin da littafan Shi’ah suka ce:-
Babban malamin Shi’ah Al-Fadhlu Bin Hasan At-Tabarisy wanda ya rasu a 548 H ya ruwaito a cikin littafinsa I’ilaamul Waraa Bi A’alaamil Hudaa 1/412, da Malamin Shi’ah Muhammad Bin Aliy Bin Shar Ash’wab wanda ya mutu a 588 H ya ruwaito a cikin littafinsa Manaaqibu A’ali Abi Taalib 3/185, da Malamin Shi’ah Ibnu Abil Fathil Irbiliy wanda ya mutu a 693 H ya ruwaito a cikin littafinsa Kashful Gummah 2/142, da Malamin Shi’ah Haashimul Bahraaniy wanda ya mutu a 1,107 H ya ruwaito a cikin littafinsa Madinatu Ma’ajizil A’immah 3/256, da Malamin Shi’ah Muhammad Baaqir Al-Majlisiy wanda ya mutu a 1,111 H ya ruwaito a cikin littafinsa Bihaarul Anwar 43/298, da Malamin Shi’ah Aliyyun Namaaziy Ash-Shaaharuudiy wanda ya mutu a 1,402 H ya ruwaito a cikin littafinsa Mustadraku Safeenatil Bihar 5/281, dukkan wadannan Manyan malaman Shi’ah sun ruwaito cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce wa jikansa Sayyidina Hasan Bin Aliy:-
((ان ابني هذا سيد ولعل الله ان يصلح به بين فئتين عظيمتين من المسلمين)).
Ma’ana: ((Lalle wannan da nawa shugaba ne, ina tsammanin Allah Zai sulhunta tsakanin manyan bangarori biyu na Musulmai ta hanyar shi)).
(5). Lalle ‘yan bidi’ah sun tabe da suka maida zagin Sayyidina Mu’awiyah da la’antar shi da yin masa sharri da yarfe wani ginshiki daga cikin ginshikan adrininsu. Tabbas sun tabe saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya haramta zagin Musulmai umuuman, ya kuma haramta zagin Sahabbansa khusuusan.
– Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 48, da Muslim Hadithi na 64, da Tirmiziy Hadithi na 1983, da Nasaa’iy Hadithi na 4108, da Ibnu Majah Hadithi na 69, da Ahmad Hadithi na 3647, da Ibnu Hibban Hadithi na 5939, da Bazzar Hadithi na 1172, da Dabaraaniy Hadithi na 9958 daga Sahabi Abdullahi Bin Mas’ud Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((سباب المسلم فسوق وقتاله كفر)).
Ma’ana: ((Zagin Musulmi fasikanci ne yakar shi kuma kafirci ne)).
– Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3673, da Muslim Hadithi na 2540, da Abu Dawud Hadithi na 4660, da Tirmiziy Hadithi na 3861, da Nasaa’iy Hadithi na 8250, da Ibnu Majah Hadithi na 161, da Ahmad Hadithi na 11094, da Ibnu Hibban Hadithi na 7353, da Dabraaniy cikin Kabeer Hadithi na 303 daga Sahabi Abu Sa’id Al-Khudriy, da Sahabi Abu Hurairah Allah Ya Kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((لا تسبوا أصحابي فَلَو ان احدكم أنفق مثل احد ذهبا ما بلغ مد احدهم ولا نصيفه)).
Ma’ana: ((Kada ku zagi sahabbaina lalle da dayanku zai ba da sadakar zinarin da ya kai dutsen Uhudu nauyi to da ladan da zai samu ba zai kai ladan da dayansu zai samu ba idan ya yi sadakar mudu guda ko ma rabin mudun da zai ciyar)).
-Imamud Dabraaniy ya ruwaito cikin Kabeer Hadithi na 12,541, da Bazzar cikin Musnad Hadithi na 5753 daga Sahabi Ibnu Abbas da Sahabi Ibnu Umar Allah Ya kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((من سب أصحابي فعليه لعنة الله والملائكة والنَّاس اجمعين)).
Ma’ana: ((Duk wanda ya zagi Sahabbaina tsinuwar Allah da Mala’iku da Mutane gaba daya ta tabbata a kan shi)).
(6) Ina kalubalatar dukkan Rafidhawa da su kawo wa Duniya wani hadithi sahihi da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi nassi a cikinsa cewa: Mu’awiyah kafiri ne, ko Mu’awiyah munafuki ne, ko Mu’awiyah dan Wuta ne.
(7) Lalle Ahlus Sunnah sai su gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya hore musu mika wuya ga dukkan abin da Allah da MsnzonSa suka ce musu, ko suka umurce su da yi ko da bi. Allah Ya taimake mu. Ameen.
Masha Allah, Allah yakarawa Dr lafiya
Hey people!!!!!
Good mood and good luck to everyone!!!!!
Thank you for your sharing. I am worried that I lack creative ideas. It is your article that makes me full of hope. Thank you. But, I have a question, can you help me?