HUKUNCIN KARBAR KYAUTAR IDIN KIRSIMETI DA CIN ABINCIN WANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA’LIH SUKA YI BAYANI

1- Da yake gobe laraba ne Kiristoci za su fara abin da suke kira bukin kirsimeti (idin kirsimeti) wanda wasu Kiristocin suke yin sa a ranar 25/12 watau ishrin da biyar ga watan December, wasu kuwa suke yin sa a ranar 7/1, watau ranar bakwai ga watan January.
2- Sannan da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin su Kiristoci da kuma al’ummar Musulmi.
3- Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai.
4- Sannan da yake akwai masu bidi’ah da dama da ke halatta abin da Shari’ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari’ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al’ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al’ummar Musulmi.
**************************
To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-

Na farko: Shi dai bukin kirsimeti wata bidi’ah ce da bata da kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta -kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi’ar idin mauludi- Kiristoci sun kirkiri wannan bidi’ar ce kuwa a shekarar miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.

Na biyu: Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih -Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’uttaabi’in- dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqii ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
‎((اجتنبوا أعداء الله في عيدهم)). انتهى.
Ma’ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)). Intaha.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa Misriyyah1/517 :-
‎((وليس للمسلمين ان يعينوهم على أعيادهم لا ببيع ما يستعينون به على عيدهم ولا باجارة دوابهم ليركبوها في عيدهم لان أعيادهم مما حرمه الله تعالى ورسوله صلى الله عليه وسلم لما فيها من الكفر والفسوق والعصيان)). انتهى.
Ma’ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu cikin idodinsu, ko  dai ta hanyar sayar musu da abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)). Intaha.

Na uku: Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam suka yi sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin zuwa mazhabobi biyu:-

Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar da Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan bangarorin Kiristoci ke bi.

Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da bangarorin Orthodox ke bi.

Na hudu: Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke kafurai, babu sabani cikin wannan mas’ala cikin  shari’ar Musulunci.

Na biyar: Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa, da Kiristoci, su wannan nau’i na kafurai Musulunci ya halatta wa Musulmi cin yankansu, da kuma auren matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran addinai na bautan gumaka.
*************************
Idan Musulmi sun fahimci wannan sai mu shiga bayanin mas’alarmu da muke son yi wa jama’a bayaninta, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya taimake mu.

HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:

Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na kafurci da bidi’ah sun kasu kashi biyu ne:-

Na farko: Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da tufafi, da kayan marmari da sauransu.

Na biyu: Kyaututtukan da suke nama ne da ke bukatar a yi masa yanka irin ta Shari’ah.

To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari’ah, babu sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya saninmu- cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-

1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga Muhammad Dan Siiriin cewa:-
((أتي علي رضي الله بهدية النيروز، فقال: ما هذه؟ قالوا: يا امير المؤمنين هذا يوم النيروز. قال: فاصنعوا كل يوم فيروز)). انتهى.
Ma’ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa’lib Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz, sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka ce: Ya Amirar Muu’miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)). Intaha.

2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu Raa’huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga Qaa’bus Bin Abi Zabyan  daga shi mahaifin nasa cewa wata mace ta tambayi Nana A’isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((ان لنا اكارا من المجوس وانه يكون لهم العيد فيهدون لنا، فقالت: اما ما ذبح لذلك اليوم فلا تأكلوا ولكن كلوا من أشجارهم)). انتهى
Ma’ana: ((Muna da ‘yan kodago daga cikin Majusawa, sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci daga ‘ya’yan itatuwansu)). Intaha.

3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
‎((كان له سكان مجوس فكانوا يهدون له في النيروز والمهرجان فكان يقول لأهله: ما كان من فاكهة فكلوا وما كان من غير ذلك فردوه)). انتهى.
Ma’ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba hakan ba, to ku mayar da ita)). Intaha.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
‎((فهذا يدل على انه لا تأثير للعيد في المنع من قبول هديتهم، بل حكمها في العيد وغيره سواء؛ لانه ليس في ذلك إعانة لهم على شعائر كفرهم)). انتهى.
Ma’ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a’a hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba, saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin karban kyautarsu)). Intaha.

TALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa suka yi domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai  sun hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a’a an hana cin yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci to ba a cin yankansa.

HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU SABODA YIN BUKUKUWAN IDINSU:

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka saboda bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-
‎((وانما يجوز ان يؤكل من طعام اهل الكتاب في عيدهم بابتياع او هدية او غير ذلك مما لم يذبحوه للعيد. فأما ذبح المجوس فالحكم فيها معلوم فإنها حرام عند العامة. وأما ما ذبحه اهل الكتاب لاعيادهم وما يتقربون بذبحه الى غير الله نظير ما يذبح المسلمون من هداياهم وضحاياهم متقربين بها الى الله تعالى، وذلك مثل ما يذبحون للمسيح والزهرة، فعن احمد روايتان: اشهرهما في نصوصه: انه لا يباح اكله وان لم يسم غير الله تعالى. ونقل النهي عن ذلك عن عائشة وعبد الله بن عمر…..والرواية الثانية ان ذلك مكروه غير محرم)). انتهى.
Ma’ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko wanin haka. Amma abin da Majusawa suka yanka hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah’ kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A’isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)). Intaha.

Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/559 :-
((ونقلت الرخصة في ذبائح الأعياد ونحوها عن طائفة من الصحابة رضي الله عنهم، وهذا فيما اذا لم يسموا غير الله، فان سموا غير الله في عيدهم او غير عيدهم حرم في اشهر الروايتين، وهو مذهب الجمهور، وهو مذهب الفقهاء الثلاثة فيما نقله غير واحد، وهو قول علي بن ابي طالب وغيره من الصحابة، وهو قول اكثر فقهاء الشام وغيرهم. والثانية: لا يحرم وان سموا غير الله، وهذا قول عطاء ومجاهد ومكحول والاوزاعي والليث)). انتهى.
Ma’ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin mas’alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha’un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa’lib da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa’riyah, da Ubaa’dah Dan Saa’mit, kuma shi ne maganar maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa’u, da Mujaa’hid, da Makhuul, da Auzaa’ii, da kuma Laith)). Intaha.

Taliki na farko:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da suka gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne zuwa kashi biyu:-

Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah yayin yanka shi.

To ita tabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cinta.

Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma tare da nuna kyama.

Mazhaba ta biyu: Nana A’isha, da Abdullahi Dan Umar, da kuma Maluman Hanaa’bilah sun ce cin wannan nama haramun ne.

Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta, wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin wannan dabbar:-

Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba, wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa’lib, da Abud Dardaa’u, da Abuu Umamah, da Irbadh Da Saa’riyah, da Ubaa’dah Dan Saa’mit, da Hanafiyyah, da Malikiyyah, da Shafi’iyyah, da Hanaa’bilah, da mafi yawan maluman kasar Sham, suk fada.

mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan shi ne abin da Ataa’u, da Mhjaa’hid, da Makhul, da Auzaa’ii, da Laithu Dan Sa’ad, da kuma Imam Ahmad cikin ruwaya suka fada.

Taliki na biyu:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da suka gabata cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da hannayensu idan Kiristoci suka saya suka dafa a matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare shi. Wallahu A’alam.
****************************
HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:
A karshen wannan makala tamu za mu yi bayanin mene ne mash’hurin mazhabar Malikiyyah game cin yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda Musulmin wannan kasa tamu Nigeria su kara fahimtar irin banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce cikin littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma abin da wasu jahilan ‘yan bidi’ah da suke ikirarin cewa su masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne kawai suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu suka ce to shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da sharrin Shaidan.
Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya ce cikin littafinsa Aljaami’u Li Ahkaamil Qur’an 6/53:-
‎((وقال جمهور الامة ان ذبيحة كل نصراني حلال سواء من بني تغلب او غيرهم، وكذلك اليهود)).
Ma’ana: ((Jumhuurin Al’ummah sun ce: Lalle yankan ko wane kirista halal ne, babu banbanci daga kabilar Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su ma Yahudawa)). Intaha.
Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil shafi na 90
‎((وان سامريا او مجوسيا تنصر وذبح لنفسه مستحله، وان اكل الميتة ان لم يغب))
Ma’an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da yake halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda kuwa yana halatta cin mushe ne, matukar dai musulmi na sane da cewa shi din ne ya yi yankan)).
Sannan ya zo cikin littafin Adhalulu Madaarik 2/92:-
‎((يجوز للمسلم نكاح حرائر اهل الكتاب .. وكان الصحابة بتزوجون من اليهود والنصارى كثيرا زمن الفتح .. ونكح عثمان نصرانية، ونكح طلحة يهودية)).
Ma’ana: ((yana halatta ga musulmi auren ‘yantattun matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun kasance da yawa suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a lokacin da ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina Uthman ya auri wata kirista, Sayyidina Talhah ya auri wata bayahudiya)).
***********************
Muna rokon Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta Ya kuma nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ameen.

36 Comments

  1. After browsing this site, I felt invigorated, reminiscent of the thrill during the famous Running with the Bulls in San Fermin, Spain. The bold visuals and adrenaline-infused content inspire me to embrace the excitement of life’s adventures.
    I invite you to sit back and explore my website buy certified diploma
    Bye for now, and may your soul find the solace it craves

  2. Адвокат по недвижимости и жилищным вопросам играет ключевую роль в защите прав граждан в сфере жилищного законодательства, где множество нюансов иногда становится непреодолимым препятствием для обывателя. Эти специалисты не только помогают в решении споров, связанных с куплей-продажей недвижимости, но и осуществляют юридическую помощь при аренде, приватизации и других жилищных сделках. К юристу по жилищным вопросам следует обращаться при возникновении проблем с нерадивыми соседями, при необходимости оспорить решения органов власти или защитить свои права на наследуемую собственность. Адвокат по недвижимости и жилищным вопросам способен предложить профессиональную оценку ситуации, разработать стратегию защиты интересов клиента и представлять его интересы в судебных инстанциях. Компетентный юрист поможет грамотно подготовить все необходимые документы, обеспечив тем самым выполнение всех формальностей, что особенно важно в области жилищного права, где ошибки могут стоить много времени и денег. Не стоит забывать, что профессиональная поддержка необходима не только в конфликтных ситуациях, но и для предотвращения юридических проблем, что еще раз подчеркивает важность обращения к адвокату по недвижимости и жилищным вопросам при любых затруднениях.

    Еслив вам требуется помощь юриста по жилищным вопросам , рекомендую выбирать квалифицированного специалиста, он тщательно изучит вашу ситуацию и обеспечит защиту ваших прав и интересов.

  3. [url=https://centr-sadovoda.ru]Порно чат рулетка бесплатно, без регистации[/url]
    [url=https://centr-sadovoda.ru] Дешовые проститутки Оренбурга[/url]

  4. steam will send you: SMS-cipher for identification [url=https://authenticatorsteam.com/]steam desktop authenticator не работает подтверждение[/url]. Enabling steam guard mobile authenticator is a simple process that is significant increases security of your of your record.

  5. Предлагаем ознакомиться завем получить 350 000 руб от государства на свой бизнес ? [url=https://vk.link/testirovanie_na_soc_kontrakt_msp]Тест на соцконтракт 2024[/url] новые правила 2024 года: обязательный тест на мсп – узнай вопросы и ответы заранее. всего 200 руб. и ты подготовлен к тестированию! .

  6. {especially for|for} {those users|users|people}, {willing|aspiring|who wish|who want|who strive} to compare bonuses similar to {casino|gambling site|institution} with #file_links[“C:\Users\Admin\Desktop\file\gsa+en+100neonix-casino.co.ukP2URLBB.txt”,1,N], we {use|developed|created|made} a unique bonus comparison block, {in order to {facilitate|simplify} the viewing of offers from other major operators of {online|Internet|virtual} casinos.

  7. Browsing this site felt like a sensory journey through the forests of Borneo, where the lush green visuals and dynamic design evoke the richness of the rainforest. Each interactive element feels like discovering a new species in this biodiverse paradise, engaging my curiosity at every turn. The owner is likely a nature lover, sharing the wonders of the world’s ecosystems in a beautifully crafted digital experience.

    You might come across my site iNfORmaTiOn About bAuxiTES

  8. Hi, Neat post. There is an issue with your site in internet explorer, could check thisK IE nonetheless is the marketplace chief and a huge part of other folks will leave out your magnificent writing due to this problem.

  9. [url=https://hi-tech-fx.com/MetaTrader4_2025_en.pdf]MetaTrader4[/url] Selling a Brokerage Company Forex. Selling on MetaTrader4 Server and MetaTrader4 License. Forex brokerage equipment software is for sale at a price of only 0.1522 BTC The Bitcoin rate is growing, and our prices are decreasing. Selling MetaTrader4 Server at a price of 9900 euros Selling MetaTrader4 License from 3 euros https://hi-tech-fx.com/

    Skype: hi-tech-fx

  10. Прошу прощения, что я вмешиваюсь, но мне необходимо немного больше информации.
    I got to know the beta tester of virtueel telefoonnummer in order to go to the online operation and technical support of virtueel [url=https://westernwind.proboards.com/thread/184/telegram?page=1&scrollTo=218]telegram zonder telefoonnummer[/url] independently.

  11. Согласен, очень полезная фраза
    1:31; см. Быт. пол). Это основа христианства: физическое творение и человеческое тело – качественные устройства, [url=https://blackrose.com.ua/krematsija-v-zaporozhe]https://blackrose.com.ua/krematsija-v-zaporozhe[/url] созданные добрым Богом.

  12. Вас посетила просто отличная идея
    Совершайте простые и безопасные платежи посредством apple pay, paypal, [url=https://polonne.moy.su/forum/26-2227-1]https://polonne.moy.su/forum/26-2227-1[/url] venmo и кредиток.

  13. Согласен, эта замечательная мысль придется как раз кстати
    next you have the opportunity connect to [url=https://slothana-coin.com/]https://slothana-coin.com/[/url] by following the following actions. it gives traders with a simple visual method to understand dynamics of the market and definitions of whether exists greater demand or supply.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *