Babu laifi cikin yin abin da ake kira: Pre-Khudubah a ranar juma’a, inda wani malami zai rika yi wa mutane wa’azi, idan limam ya shigo domin hawa minbari sai ya daina wa’azin ya zauna. Babu laifi cikin yin hakan saboda hadithi na 374 da Imam Hakim ya ruwaito cikin Mustadrak cewa: ((Sahabi Abu Hurairah Allah ya kara masa yarda, ya kasance yana tsayuwa a ranar juma’a a gefen mimbari yana mai sanya igiyoyin takalmansa cikin dantsen hannunsa, yana kuma rike da gwafar mimbari, yana cewa: Abul Qasim Mai tsira da amincin Allah ya ce, Muhammad Mai tsira da amincin Allah ya ce, Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce, Mai gaskiya Abin gaskatawa mai tsira da amincin Allah ya ce. Daga nan kuma sai ya rika cewa cikin sashin hakan: Azaba ta tabbata ga Larabawa na sharrin da ya kusanto”. Toh idan ya ji motsin kofar ofishin Liman domin fitowar shi Liman sai ya zauna)).
((كان أبو هريرة يقوم يوم الجمعة إلى جانب المنبر فيطرح أعقاب نعليه في ذراعيه ، ثم يقبض على رمانة المنبر ، يقول : قال أبو القاسم صلى الله عليه وسلم ، قال محمد صلى الله عليه وسلم : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : قال الصادق المصدوق صلى الله عليه وسلم ، ثم يقول في بعض ذلك : ” ويل للعرب من شر قد اقترب ” فإذا سمع حركة باب المقصورة بخروج الإمام.