Ginshikin addinin Shi’ah shi ne: kushe wa Sahabbai da kafirta su, da kuma tsarkake Aliyyu Bin Abi Talib da wasu kadan daga cikin ‘ya’yansa da jikokinsa, da kuma diyar Annabi daya tak, watau Fatimah, banda sauran ‘ya’yan nasa mata.
Shi’ah su kan yi amfani da duk wata ‘yar dama da za su samu domin karfafa wannan ginshiki na addinin nasu; kafirta Sahabbai da kuma tsarkake wasu ‘yan kadan daga cikin Ahlul Baiti.
Sai dai kuma yana da wahala Shi’ah Rafidah su bayar da wata hujja domin karfafa wannan akidar tasu ba tare da ka ga cewa akwai abin da ke warware manufarsu ba a cikin hujjar .
Misali: Sau da dama ne Shi’ah suke ambaton kissar رزية الخميس domin kushe wa Umar da kafirta shi, to amma in ka dubi kissar da kyau sai ka ga cewa: ai shi ma Aliyyu Bin Abi Talib din abin kushewa ne a cikin kissar; domin kuwa shi ma yana gurin a lokacin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce musu dukkansu: هلم اكتب لكم كتابا لا تضلوا بعده tarjama: “Ku kawo mini abin rubutu in rubuta muku littafin da ba za ku bace ba a bayansa”.
Shi dai Umar Bin Khattab babu abin da ya ce a lokacin da Annabi mai tsura da amincin Allah ya bayar da wannan umurni face: ان النبي قد غلب عليه الوجع وعندكم القرءان حسبنا كتاب الله tarjama: “Lalle zafin ciwo ya ci karfin Annabi, to amma Alkur’ani na gurinku, littafin Allah ya ishe mu”, abin da Umar ya fada ke nan babu inda ya kama hannun wani ya hana shi kawo wa Annabi abin rubutu, ko kuwa wani ya kawo abin rubutun sannan ya kwace ya hana shi kaiwa ga Annabi mai tsira da amincin Allah.
To amma kuma shi ma Ali Bin Abi Talib yana gurin, kuma Annabi ya ce ne: Ku kawo mini” kun ga umurnin ya shafi kowa da kowa ne, in kuwa haka ne don mene ne shi Ali Bin Abi Talib din bai bi umurnin ba ya je ya kawo wa Annabi abin rubutun?? Dole ne ‘Yan Shi’ah su ba da amsar wannan tambaya.
Littatrafan Shi’ah sun tabbatar da cewa Ali da Abbas da Fadhl dukkansu uku suna gurin. Ga ma abin da الشيخ المفيد محمد بن محمد بن النعمان العكبري البغدادي wanda ya mutu a shekarar hijira ta 413 yake cewa cikin littafinsa الارشاد في معرفة حجج الله على العباد mujalladi na daya shafi na 184: “٠٠٠ فلما افاق صلى الله عليه وءاله قال بعضهم الا ناتيك بكتف يا رسول الله ودواة؟ فقال: ابعد الذي قلتم لا ولكنيي اوصيكم باهل بيتي خيرا ثم اعرض بوجهه عن القوم فنهضوا وبقي عنده العباس والفضل وعلي بن ابي طالب ٠٠٠”
A nan idan har Umar ya yi laifi da bai kawo wa Annabi abin rubutu ba, to shi kuma Ali mene ne ya yi tun da shi ma bai kawo wa Annabi abin rubutun ba??
Maganar kuwa da Umar ya yi ta cewa: Zafin ciwo ya ci karfin Annabi gaskiya ce”; domin kuwa Annabi yana suma ne ya farfado, yana suma ne ya farfado.