1. Babu wani abu da ake kira karancin sadaki a cikin ingantacciyar sunnar Annabi mai tsira da aminci.

2. Mu a nan Nigeria duk abin da ma’aurata suka yi ittifaki a kan shi na kudin Naira komin karancinsa toh tabbas ya halatta a matsayin Sadaki.

3. Lalle Malaman da suka ce: Ba ya halatta sadaki ya kasa Rubu’u dinar, ko ya kasa Nisfu dinar, ko ya kasa Dirhami uku, ko ya kasa Dirhami biyar, ko ya kasa Dirhami goma, ko ya kasa Dirhami hamsin. Dukkansu ijitihadinsu ne kawai suka fada amma ba wai nassin Alkur’ani ko nassin ingantaccen hadithi ba ne suka zo da hakan.

4. Gaskiyan al’amari shi ne Sadaki ba yi da iyaka a yawa, haka nan ba yi da iyaka a karanci; domin Annabi mai tsira da aminci ya daura wa wani Sahabi aure a kan karatun Kur’ani da zai koya wa matar; saboda ba yi da ko kobo daya da zai bayar a matsayin Sadaki. Haka nan Annabi mai tsira da aminci ya yi yunkurin daura aure a kan zoben bakin karfe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *