Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa’iqamatis Sunnah ƙarƙashin Jagorancin Sheikh (DR) Imam Abdullahi Bala Lau ta kai ziyarar jaje ga Al’ummar Maiduguri bisa ib’tila’in ambaliyar ruwa data shafe su.

Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa Sheikh Bala Lau, a madadin Ƙungiyar na tarayyar Nigeria ta jajantawa Mutanen Maiduguri bisa wannan babbar ib’tila’i data same su na ambaliyar ruwa kuma yace wannan jarrabawace daga Allah.



Ƙungiyar ta gabatar da tallafin Shinkafa Tirela ɗaya mai ɗauke da Buhu ɗari bakwai (700)  ga Al’ummar Jihar domin rage musu raɗaɗin wannan ib’tila’i.

Ƙungiyar ta samu tarba daga Gwamnan Jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum, kuma ya yabawa Ƙungiyar bisa ga wannan ziyara da kuma tallafin da Ƙumgiyar ta bayar, ya kuma bayyana cewa In shaa za’a raba wannan tallafi ga Al’ummar da ib’tila’i ta shafa bisa Adalci.

Daga ƙarshe Ƙungiyar ta ziyarci fadar mai Martaba Shehun Borno inda ta jajenta mishi a madadin Ƙungiyar kuma aka gabatar da Addu’oi na musamman.

Daga cikin manyan Maluma da suka marawa Shugaban baya sun haɗa da, Shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sheikh (DR) Muhammad Kabiru Haruna Gombe Sakataren Ƙungiya na ƙasa, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Engr. Mustapha Imam Sitti Director Agaji na Ƙasa, Alaramma Ahmad Ibrahim Sulaiman Kano, Alaramma Nasiru Salihu Gwandu, H.E Sani Abubakar Ɗanladi, Engr. Salisu Gombe Shugaban Jibwis Gombe, Ibrahim Baba Sulaiman Director Jibwis Social Media na Ƙasa da sauran su.

3 Comments

  1. Keep up the fantastic work! Kalorifer Sobası odun, kömür, pelet gibi yakıtlarla çalışan ve ısıtma işlevi gören bir soba türüdür. Kalorifer Sobası içindeki yakıtın yanmasıyla oluşan ısıyı doğrudan çevresine yayar ve aynı zamanda suyun ısınmasını sağlar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *