La’antar mutumin da ya cancanci a la’ance shi halal ne a Shari’ar Musulunci. Su kuma laifukan da suke halattar da a la’anci mutum namiji, ko mace guda uku ne, kamar haka:-

1. Kafurci, dalili shi ne Allah Madaukakin Sarki Yana cewa cikin surar Ahzab aya ta 64:
ان الله لعن الكافرين واعد لهم سعيرا
ma’ana: ((Lalle Allah Ya tsine wa Kafurai, Ya kuma Yi musu tattalin Sa’ira)). Akwai wasu nassoshin ma banda wannan.

2. Fasikanci, watau barin hanyar Shari’a, dalili shi ne: Ahmad ya ruwaito hadithi na 7083, da Ibnu Hibban: 5753, da Hakim: 8346, da Tabrani: 1439 da isnadi mai kyau daga Dan Amru ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:
((سيكون في ءاخر امتي رجال يركبون على سروج كأشباه الرحال ينزلون على أبواب المساجد نساءهم كاسيات عاريات على رؤوسهن كاسنمة البخت العجاف العنوهن فإنهن ملعونات)).
Ma’ana: ((Za a sami wasu mazaje cikin al’ummata a karshen zamani za su rika hawan Sirdodi masu kama da kekunan dawaki suna sauka kofofin masallatai, matansu kuma suna sanye da sutura amma kuma a tsiraice suke, kayunansu kuma ka ce tozayen rakuman nan ne masu tozo biyu ramammu. Ku la’ance su lalle su matan la’anannu ne)). Sanna Buhari ya tuwaito hadithi na 6783, da Muslim: 1687 daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:
((لعن الله السارق يسرق البيضة فتقطع يده ويسرق الحبل فتقطع يده)).
Ma’ana: ((Allah Ya la’anci Barawo, ya saci kwai, ko ya saci makami a yanke hannunsa. Ya saci Igiya a yanke hannunsa)). Haka nan Muslim ya ruwaito hadithi na 1978 daga Aliyyu Dan Abi Talib ya ce Manzon Allah mai tsira da mincin Allah ya ce: ((لعن الله من غير المنار)). Ma’ana: ((Allah Ya la’anci wanda ya jirkita kan iyaka)). Akwai wasu nassoshin ma banda wadannan.

3. Bidi’ah, dalili shi ne Magabata da yawa ne suka la’anci ayyanannun ‘yan bidi’ah.
– Abdullahil Harawiy ya ruwaito cikin littafinsa Zammul Kalami wa Ahlihi athari na 1020 cewa Abu Hanifa ya ce:
((لعن الله عمرو بن عبيد فانه فتح للناس الطريق الى الكلام فيما لا يعنيهم من الكلام)).
Ma’ana: ((Allah Ya la’anci Amru Bin Ubaid, lalle ya bude wa mutane hanyar yin magana game da abin da bai shafe su ba na magana)).
– Har yanzu Abdullahil Harawiy ya ruwaito cikin Zammul kalami wa Ahlihi athari na 860 cewa Abdurrahman Bin Mahdiy yana cewa:
((دخلت على مالك وعنده رجل يسأله عن القرءان فقال: لعلك من اصحاب عمرو بن عبيد؟ لعن الله عمرا فانه ابتدع هذه البدع من الكلام)).
Ma’ana: ((Na shigo gurin Imam Malik na tarar da wani mutum yana tambayar shi game da Alkur’ani, sai ya ce: Watakila kana daga cikin almajiran Amru Bin Ubaid? Allah Ya la’anci Amru; domin shi ne ya kirkiro wadannan bidi’o’i na Kalam)).

– Abdullah Bin Ahmad ya ruwaito cikin littafinsa Assunnah athari na 189 daga Yazid Bin Harun cewa ya ce: ((لعن الله الجهم ومن قال بقوله)). Ma’ana: ((Allah Ya la’anci Jahmu da duk wanda ya bi maganarsa)).

– Sannan Ahmad Bin Abdillah Al-Ijliy ya ce a cikin littafinsa Ath-Thiqat athari na 159:
((رأيت بشر المريسي عليه لعنة الله مرة واحدة شيخا قصيرا دميم المنظر …)).
Ma’ana: ((Sau daya tak na ga Bishir Al-Mirriisiy wani tsoho gajere mai mummunar fiska..)). Akwai wasu maganganun Salaf cikin wannan babin banda ma wadannan.

A karshe, idan har Allah Ya sa aka fahimci wannan bayani namu, to za a fahimci cewa duk wani nassi da yake haramta la’ana, to yana haramta la’antar wanda Shari’ah ba ta halatta la’antar shi ba ne. Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *