Shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa JIBWIS NIGERIA Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya sauka garin Gombe domin halartar Auren Ƴar sakataren Kungiyar na Ƙasa Sheikh Kabiru Haruna Gombe inda ya sauƙa gidan Sheikh Usman Isa Taliyawa.
Kungiyar zata gabatar da gagarumin Wa’azin walima a yau ɗinnan inda ake saran halartan manyan Maluma daga ciki da wajen Nigeria 🇳🇬.
Muna fata Allah Ta’aa’laa ya sanya Albarka mai yawa a cikin wannan Aure yasa ayi taro lafiya a gama lafiya.