1. Ni dai a yanzu ina ganin cewa babu abin da ya rage wa masu nuna shakku متشككون daga cikin ‘yan bidi’ah, da kuma ‘yan a’adifah, da kuma jahilai ‘yan hayaniya, face su rika yin wannan shakka tasu cikin dukkan wani abu da suka gani a cikin Alkur’ani mai girma, ko a cikin ingantattun hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, wanda yake sam bai kwanta musu cikin zuciyarsu ba, bai kuma kama hankulansu ba! Ina ganin babu abin da ya rage musu face su rika yin hakan tunda yake babbar madogara a gurinsu ita ce son zukatansu!

2. Saboda haka duk wani nassin suna, ko nassin jumlar da bai kwanta musu cikin zukatansu ba, toh kuwa dole ne su yi ta masa ta’awili التأويل su kuma yi ta kawo masa ihtimalat الاحتمالات domin su a gurinsu a bin da zai kwanta musu a cikin zuciyarsu ne kawai zai iya kasacewa addin gaskiya, ko zai iya kasancewa labarin gaskiya!!  Misali: a duk lokacin da suka ga an rubuta lafazin Muhammad, ko suna Muhammad a cikin Alkur’ani mai girma, ko a cikin ingantattun hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah suna iya yin  shakkarsa, suna iya kawo ihtilamin cewa zai iya kasancewa ba Muhammad Dan Abdullahi ba ne, a’a zai iya kasancewa Muhammad Bin Sufyan Bin Mujashi’i محمد بن سفيان بن مجاشع ne ake nufi, ko kuwa a’a Muhammad Bin Uhaihah Bin Hallaj محمد بن أحيحة بن الحلاج ne ake nufi, ko kuwa Muhammad Bin Hamran Bin Rabi’ah محمد بن حمران بن ربيعة ne ake nufi; domin kuwa dukkan wadannan mutum uku mutane ne wadanda Quraishawa suka sanya wa suna Muhammad a zamanin Jahiliyyah -kamar yadda babban malamin Sirah أبو القاسم عبد الرحمن بن عبد الله السهيلي ya rubuta a cikin littafinsa na Sirah mai suna الروض الأنف في شرح السيرة النبوية لابن هشام (Ar-Raudhul Unuf)- tunda kuwa ko wanne daga cikin wadannan mutum uku sunan shi Muhammad ne, toh kuwa tana iya yiwuwa shi ake nufi ba waninsa ba!!

3. Haka nan dukkan wasu muhimman batutuwa da suka zo cikin Alkur’ani mai girma, da kuma ingantattun hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah masu daraja toh wadannan Mutashakkikun متشككون suna iya yi masa ta’awili التأويل suna iya ba shi ihtimalat الاحتمالات daban daban, ta yadda za su mayar da addinin gaba dayansa tamkar wasan yara iyazan billah!!

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *