Shari’ar Musulunci sai da ta fara tsarkake Manzon Allah da Matayensa tukun cikin Nassin Alkur’ani mai girma, kafin ta tsarkake Nana Fadimah da Sayyidina Aliyyu da ‘ya’yansu Hasan da Husaini da Nassin hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Watau bayanin tsarkakar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da Matayensa Uwayen Muminai ya zo ne cikin nassin Alkur’ani mai girma, amma bayanin tsarkakar ‘yarsa Fatimah da Jikokinsa Hasan da Husain da dan Baffansa Aliyyu ita wannan ta zo ne cikin Nassin Riwayar Hadithi watau Hadithin Kisa’i da aka sani.
Ga Nassin Alkur’ani mai girman nan da ya tsarkake Matayen Manzon Allah tare da shi kansa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah daga Suratul Ahzab ayah ta 32-34:-
{يا نِساءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّساءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا (32) وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجاهِلِيَّةِ الْأُولى وَأَقِمْنَ الصَّلاةَ وَآتِينَ الزَّكاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّما يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا (33) وَاذْكُرْنَ ما يُتْلى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آياتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ إِنَّ اللَّهَ كانَ لَطِيفًا خَبِيرًا (34)}.
Tarjama: ((Ya ku matan Annabi ba kamar sauran Mata kuke ba idan kuka yi takawa, kada ku karairaye sauti har wannan da cuta ke cikin zuciyar ya yi tsammani, ku fadi magana sananniya. Ku lazimci gidajenku, kada ku rika bayanar da adonku irin bayyanarwar Jahiliyyar farko, ku tsayar da Salla, ku bayar da Zakka, ku yi wa Allah da ManzonSa biyayya; abin sani shi ne Allah na son tafiyar muku da dauda ya ku Ahlul Bait, kuma Ya tsarkake ku tsarkakewa. Ku tuna da abin da ake karantawa a cikin gidajenku na ayoyin Allah da Hikimah, lalle Allah Ya kasance Masanin kwakwaf ne Mai bayar da labari)).
Ku lura za ku ga dukkan lamirai da suke cikin ayoyin nan 3 lamirai ne abokin magana, watau مخاطب ba wai lamirai ba ne na wanda ake magana a kansa, watau غائب . Ga lamiran kamar haka: لستن، ان اتقيتن، فلا تخضعن، وقلن، وقرن، في بيوتكن، ولا تبرجن، وأقمن، وءاتين، وأطعن، عنكم، ويطهركم، واذكرن، في بيوتكن. Ta yiwu wani ya ce toh mene ya sa aka yi amfani da ميم الجمع cikin عنكم da يطهركم ba ce: عنكن da kuma يطهركن ba? Amsa a nan ita ce: An yi amfani da ميم الجمع ne domin shigar da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah cikin tsarkakewar; tamkar yadda aka yi amfani da ita ميم الجمع din a cikin Suratu Hud a ayah ta 71-73, inda Allah Ya ce:-
وَٱمْرَأَتُهُ قَآئِمَةٌ فَضَحِكَتْ فَبَشَّرْنَاهَا بِإِسْحَاقَ وَمِن وَرَآءِ إِسْحَاقَ يَعْقُوبَ ﴿٧١﴾ قَالَتۡ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ ءَأَلِدُ وَأَنَا۠ عَجُوزٞ وَهَٰذَا بَعۡلِي شَيۡخًاۖ إِنَّ هَٰذَا لَشَيۡءٌ عَجِيبٞ ﴿٧٢﴾ قَالُوٓاْ أَتَعۡجَبِينَ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِۖ رَحۡمَتُ ٱللَّهِ وَبَرَكَٰتُهُۥ عَلَيۡكُمۡ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِۚ إِنَّهُۥ حَمِيدٞ مَّجِيدٞ ﴿٧٣﴾
Tarjama: ((Matarsa tana tsaye sai ta yi dariya, sai muka yi mata albishir da samun Ishaq, kuma bayan Ishaq ma akwai Yaqub. Sai ta ce: Ya kaitona! Yanzu zan haifu bayan ina tsohuwa, kuma ga mijina ma tsoho? Lalle wannan abu ne na ban mamaki. Sai suka ce: Za ki yi mamaki ne game da al’amarin Allah? Rahamar Allah da AlbarkarSa su tabbata a gareku ya ku Ahlal Baiti, lalle Shi Abin godewa ne, kuma Mai girma)).
Ku lura za ku ga cewa Allah Madaukakin Sarki Yana bayar da labarin abin da ya gudana ne a tsakanin matar Annabi Ibrahim alaihis salam tare da Mala’iku. Sannan a ayah ta uku sai Mala’iku suka koma yin magana da matar Annabi Ibrahim kai tsaye, aka kuma yi amfani da lamirin lamirai abokin magana, watau مخاطب har guda biyu: أتعجبين، da kuma عليكم a cikin عليكم sai aka yi amfani da ميم الجمع domin a shigar da Annabi Ibrahim alaihis salam, sai aka ce: رحمة الله وبركاته عليكم اهل البيت.
Toh, bayan wadannan ayoyi na tsarkake Manzon Allah da matayensa sun sauko ne cikin Suratul Ahzab sai kuma Sunnah ingantacciya ta tabbatar tsarkakar Nana Fadima da Sayyidina Ali da kuma ‘ya’yansu Hasan da Husaini Allah Ya kara musu yarda cikin hadithin Kisa’i.
Kuma wannan tsarkaka Shar’iyyah da Alkur’ani mai girma ya tabbatar wa Matayen Annabi, da kuma wacce Sunnah ta tabbatar wa Fadimah da Hasan da Husaini da Aliyyu tsarkake ce da take nufin takawa bai ismah ba kamar yadda ‘yan bidi’ah suke cewa.
Im now not certain the place you are getting your information, but great topic. I needs to spend some time studying more or working out more. Thanks for wonderful information I used to be looking for this information for my mission.
Thanks for sharing. I read many of your blog posts, cool, your blog is very good.
Thanks for sharing. I read many of your blog posts, cool, your blog is very good.
I don’t think the title of your article matches the content lol. Just kidding, mainly because I had some doubts after reading the article.