1. Wasu bayin Allah saboda kawai gwagwarmayar wane ne ya kamata ya zamanto shugaban Kasar Nigeria sun kira muslim-muslim ticket da sunan abu mara ma’ana, ko abin da aka tsara saboda kawai yaudarar Al’ummar Musulmin Arewacin Nigeria!! Lalle irin wannan magana ba za ta dace da mutum muttazini ba; sawaa’un musulmi ne shi ko kuwa wanin musulmi ne shi.
2. Idan kana son fahimtar rashin gaskiyar wannan ikirari na su wadannan masu hamayya sai ka dubi irin tsananin damuwar da kungiyar nan mai tsananin ta’assubanci ta CAN ta nuna a kan samuwar wannan muslim-muslim din.
3. Tabbas a cikin tsarin muslim-muslim ticket akwai fa’idah ko dai fa’idah maddiyyah ko kuwa fa’idah ma’anawiyyah; ke nan babu mai kore samuwar wannan Fa’idar mutlaqan sai wanda jakin gidansa ma ya fi shi hankali.
4. Sannan Mahankalta suna sane da cewa Ita fa’idah ko da ma’anawiyyah ce ita to tabbas Shari’ar Musulunci tana girmamata kuma al’ummar musulmi suna kai kawo domin tabbatar da ita; wannan shi ne ma ya sa a lokacin da Kafurai Kiristoci Rumawa Bizantawa suka yi nasara a kan Kafurai Majusawa Farisawa Masu bautar wuta sai Al’ummar Musulmi Sahabbai a garin Makkah suka yi ta yin farin ciki; dalilin farin cikinsu kuwa shi ne duk da kasancewar bangarorin biyun kafurai ne, toh amma Kafurai Ahlul Kitabi (Kiristoci ko Yahudawa) sun fi kusa da Musulmi a kan Kafurai masu bautar gumaka: Wuta ko wanin Wuta.
5. Tabbas fa’idar da Al’ummar Musulmi suka samu saboda cin nasarar da Rumawa suka yi a kan Farisawa fa’idah ce kawai ma’anawiyyah ba ma maddiyyah ba; in kuwa haka al’amarin yake toh ta kaka ne wani musulmi a nan Nigeria ko a Arewacin Nigeria zai budi baki ya ce: muslim-muslim ticket shirme ne kawai, ko kuwa yaudara ce kawai ga Al’ummar Musulmin Nigeria?? Allah muke rokon taimakonSa. Ameen.