Ni a ganina sam sam ba kiristanci da kiristoci ba ne suka dami Donald Trump ko suke cikin ajandarsa ba, a’a, babban abin da yake damunsa shi ne matsalar ƙwaƙwalwa, sam ba manufar Donald Trump ba ce taimakon kiristocin Nigeria, ko taimakon kiristanci a Nigeria, a’a manufarsa ita ce kawo hargitsi a cikin Nigeria ta yadda zai haifar da yaƙin basasa a tsakanin al’ummar musulmi da al’ummar kirista na shekaru mara iyaka.
Ku lura sosai za ku gane cewa: in da kiristanci da kiristoci ne suka dami Donald Trump to da bai uzzura wa baƙar fatar South Africa tare da shugaban ƙasarsu Cyril Ramaphosa ba; domin kuwa ai dukkansu kiristoci ne. Haka nan in da kiristanci da kiristoci ne suka dami Donald Trump toh da bai uzzura wa kiristocin ƙasar Venezuela tare da shugaban ƙasarsu Nicolas Maduro Moras ba; domin kuwa ai dukkansu kiristoci ne.
Tabbas jigo a ɗabi’ar Donald Trump shi ne: zalunci da hargitsi da hauka, kamar dai yadda tsohon shugaban America Barrack Obama ya sifanta shi a ranar asabar da ta wuce 01/11/2025 a jihar Virginia cewa: shi mutum ne mai karya doka da oda, mai sakarci da hauka a fadar mulki ta White House.
Allah Maɗaukakin Sarki muke roƙon Ya tsare mana Nigeria da al’ummarta Ya ba mu lafiya da zama lafiya tare da yelwar arziki. Ameen.
Allah Ya Sakada Alkhairi Yasa Albarka
bạo hành trẻ em“