NASIHA:
1. Yana da kyau al’ummarmu masu daraja na jihar Taraba su kara kusantar Allah Ubangijinsu, su kara karfafa niyyarsu ta yin aiki tukuru domin samar wa kansu adalci da daidaito cikin jiharsu ta hanyar Ka’ida da Shari’a.
2. Wajibi ne al’ummarmu da ake zalunta su yi watsi da dukkan wani makirci da kaidi da yake fitowa daga makiyansu masu share su a aikace daga dukkan wani hakki nasu mai muhimmanci.
3. Allah Madaukakin Sarki Ya ce a cikin Surar Taubah aya ta 10: (( لا يرقبون في مؤمن إلا ولا ذمة وأولئك هم المعتدون)) ((Game da abin da ya shafi mumini sam ba sa kimanta dangantaka ta jini, ko wani alkawari da ke tsakaninsa da su, wadannan su ne masu ketare iyaka)).