Gwamnatin jihar Plateau ta bayar da izinin shugabannin da’awar Sunnah su kafa kungiyar Izalah a ranar 13/2/1978. Kuma domin ita Gwamnatin ta bayar da shaidar izinin kafa Kungiyar ta gayyaci shugabannin jami’an gwamnatin Jihar tare da shugabannin tsaro na Jihar, da kuma shugabannin garin Jos, da su kansu shugabannin da’awar Sunnah, da shugabannin Jama’atu Nasril Islam, da shugabannin darikar Tijjaniyyah, da shugabannin darikar Kadiriyyah. Kuma dukkan wadannan bangarorin da ita gwamnatin jihar Plateau ta gayyata ta ba su kwafin takardar ba da izinin kafa ita Kungiyar.

Ga shugabannin jami’an gwamnatin jihar Plateau tare da shugabannin tsaro na Jihar da suka halarta kamar haka:
1. Gwamnan mulkin soja na Jihar Air Commodore Dan Suleiman.
2. Sakataren gwamnatin Jihar, Alhaji Kasimu.
3. Alhaji Hassan Shu’aibu.
4. Alhaji Shehu Mamman.
5. Alhaji Isma’ila Adamu.

Ga kuma dattawan garin Jos da aka gayyata kuma suka halarta kamar haka:
1. Babban Limamin garin Jos Sheikh Sa’idu Hammajam.
2. Alhaji Inuwa Aliyu.
3. Alhaji Lawal Maishuga.
4. Alhaji Abubakar Hamma.
5. Alhaji Sulanjebu.
6. Alhaji Hassan Maiwarwaro.

Ga kuma su kansu shugabannin da’awar Sunnah da aka gayyata kamar haka:
1. Alhaji Garba Fasali, wanda shi ne shugabansu.
2. Alhaji Salihu Ahmad.
3. Alhaji Musa Maigandu Muhammad.
4. Sheikh Isma’ila Idris.
5. Sheikh Imam Yahya Kaduna Vom.
6. Alkali Kabiru Adamu.
7. Alhaji Ibrahim Sulaiman.
8. Alhaji Idris Mai kaset.
9. Alhaji Salihu Namaska.
10. Alhaji Garba Kwamored.
11. Alhaji Ibrahim Gwangere.
12. Alhaji Adamu Kafinta.
13. Alhaji Yunusa Maigwanjo.
14. Alhaji Tsoho Musa.
15. Alhaji Adamu Hussaini.
16. Alhaji Idin Binta.
17. Alhaji Yahya Aga Abubakar, wanda shi ne sakatarensu.

Ga kuma shugabannin Jama’atu Nasril Islam da aka gayyata kamar haka:
1. Sheikh Abdulaziz Yusuf.
2. Sheikh Aliyu Usman.
3. Alhaji Abubakar Misau.

Ga kuma shugabannin darikar Tijjaniyyah da aka gayyata kamar haka:
1. Alhaji Salihu Nakande.
2. Alhaji Baba Dannufawa.

Ga kuma shugabannin darikar Kadiriyya da aka gayyata kamar haka:
1. Sheikh Adamu.
2. Sheikh Hashimu.

Allah Madaukakin Sarki muke rokon Ya taimake mu Ya kuma daukaka da’awar Sunnah a wannan Kasa tamu. Ameen.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *