1. Tabbas rashin fikhun Shi’ah Rafidha ga nassoshin Shari’ar Musulunci yana daya daga cikin manyan dalilan da ya sa suke ta fagauniya da dimauta cikin al’amuransu na addini.

2. Lalle ya kamata Shi’ah Rafidha su san cewa  dukkan mumini babu mai kinsa sai munafuki, babu kuma mai son sa sai mumini, toh amma wannan soyayyar, da wannan kiyayyar ana nufin na addini ne; watau ana nufin soyayya da kiyayya wanda aka yi saboda addini, ba wai saboda wata dabi’a ba, ko wani al’amari ba da ya shafi al’amuran mutane na yau da gobe ba; domin a dabi’a ta yiwu ka ga wani kafuri ko wani munafuki yana son wani mumini soyayya irin ta dabi’a, kamar a ce wani namiji kafiri ko munafuki zai yiwu ya ji yana son wata mace mumina amma soyayya ta dabi’a ba wai soyayya wacce ta faru saboda addini ba. Haka nan akasin wannan shi ma yana iya faruwa, haka kuma ita kiyayya, tana iya yiwuwa wani mumini ya ki wani mumini amma kiyayya ta dalilin dabi’a ko ta dalilin wani al’amari na yau da gobe, tabbas irin wannan kiyayya ba za ta sa daya daga cikinsu ya zama kafuri ba, ko kuwa ya zama munafuki ba.

3. Lalle babu mai son Sayyidina Aliyyu so da aka yi saboda addini sai mumini, haka nan babu mai kin Sayyidina Aliyyu ki da aka yi saboda addini sai munafuki; wannan duka gaskiya ne saboda Imamu Muslim ya ruwaito hadithi na 78 daga shi Sayyidina Aliyyu Allah ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: Babu mai son sa sai mumini, babu kuma mai kin sa sai munafuki. Ga ma nassin Hadithin kamar haka:-
((قالَ عَلِيٌّ: والذي فَلَقَ الحَبَّةَ، وبَرَأَ النَّسَمَةَ، إنَّه لَعَهْدُ النبيِّ الأُمِّيِّ صَلَّى اللَّهُ عليه وسلَّمَ إلَيَّ: أنْ لا يُحِبَّنِي إلَّا مُؤْمِنٌ، ولا يُبْغِضَنِي إلَّا مُنافِقٌ)).

4. Haka nan lalle, su ma Ansarawan Madina babu mai son su na addini sai mumini, haka nan babu mai kin su ki na addini sai muna fuki; hakan kuma ya zama gaskiya ne saboda Imamul Bukhariy ya ruwaito hadithi na 3783, da Imamu Muslim hadithi na 75, daga Sahabi Baraa Bin Azib cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Babu mai son Ansarawa sai mumini, babu kuma mai kin su sai munafuki. Ga ma yadda nassin Hadithin yake:-
((لا يُحِبُّ الأنصارَ إلا مؤمنٌ ، ولا يُبْغِضُهم إلا منافقٌ ، ومَن أَحَبَّهم أَحَبَّهُ اللهُ ، ومَن أَبْغَضَهم أَبْغَضَه اللهُ)).

5. Ya ku Shi’ah Rafidha ku lura da kyau a nan za ku fahimci cewa wannan soyayya da wannan kiyayya da ake nufi cikin wadannan Hadithai biyu ana nufin soyayya ce wacce dalilnta ya kasance na Addini, haka nan kiyayyar da ake nufi a nan ita ce  kiyayyar da ta kasance dalilinta shi ne addini; za ku iya fahimtar wannan cikin sauki idan kuka san cewa ai su Ansarawan Madinah Allah Ya kara musu yarda yana iya kasancewa a samu wasunsu sun ki wasun su amma saboda kiyayya ta dabi’a, kamar a samu wata husuma a tsakaninsu saboda wani dalili irin na yau da gobe, ita kuma wannan kiyayyar ba za ta mayar da ko wanne daga cikinsu munafuki ba ko kafuri ba. Toh kuma haka nan shi ma Sayyidina Aliyyu Allah Ya kara masa yarda yana iya yiwuwa a samu wata husuma ta shiga tsakaninsa da wani mumini amma husuma ta dabi’a, husuma ta al’amuran yau da gobe har ta kai a samu wata kiyayya ta shiga tsakaninsa da wannan muminin, toh amma tabbas ita wannan kiyayyar ba za ta sa wannan mumini ya zama munafuki ko kafiri ba; domin bai ki Sayyidina Aliyyu saboda Musuluncinsa ba, a’a ya ki shi ne saboda wata dabi’a da mu’amalar yau da gobe ta kawo.

6. Ya ku Shi’ah Rafidha, idan har kun fahimci wadannan bayanai namu da suka gabata, toh ku sani wannan shi ne ya sa yakin da ya kasance a tsakanin rundunar Sayyidina Aliyyu da rundunar Sayyidina Mu’awiyah sam ba zai sa ita rundunar Sayyidina Mu’awiyah ta kasance kafira ko munafika ba, a’a, dukkan wadannan rundunoni biyu za su ci gaba da zama Muminai kamar dai yadda Allah Madaukakin Sarki ya ce cikin surar Hujurat aya ta 9-10:-
((وَإِن طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ اقْتَتَلُوا فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا ۖ فَإِن بَغَتْ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَىٰ فَقَاتِلُوا الَّتِي تَبْغِي حَتَّىٰ تَفِيءَ إِلَىٰ أَمْرِ اللَّهِ ۚ فَإِن فَاءَتْ فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا بِالْعَدْلِ وَأَقْسِطُوا ۖ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ (9) إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ (10)).
Kun gani a nan dukkan rundunonin biyu da suke yakar juna, suke karkashe juna Allah Madaukakin Sarki Ya kira su da suna muminai; dalilin haka kuwa shi ne ko wanne ne daga cikinsu yana yakar dan’uwansa ne ba don dan’uwan nasa ya yi imani ba ne, a’a sai don saboda wani al’amari na dabi’a ne na yau da gobe ne da ya shiga a tsakaninsu.

7. Tabbas rundunar Sayyidina Mu’awiyah Allah Ya kara masa yarda ta yi yaki mai tsanani da rundunar Sayyidina Aliyyu Allah Ya kara masa yarda, toh amma kuma wannan yakin da suka yi a tsakaninsu, wannan kashe juna da suka yi a tsakaninsu sun yi shi ne ba don suna bakin ciki da imanin junansu ba ne, a’a sun yi shi ne saboda wata hamayya da dabi’a ko wani abu na al’amarin duniya, na al’amari wanda yau da gobe yake kawowa.

8. Lalle ku sani ya ku Shi’ah Rafidha rashin fahimtarku ga wannan hakika shi ne yake ta dulmuyar da ku cikin wannan bakar akidah taku ta kafurta dukkan wani mumini da ya yi wata husuma da Sayyidina Aliyyu Allah Ya kara masa yarda, wanda kuma wannan kuskure ne babba.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *